Darajar Mutum Da Cikar Kimarsa
🏽Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba.
Kada yau ta sha ma kai, domin gobe ma rana ce.
🏽Yafe wa wanda ya cuce ka ni'ima ce.
Tuna abin bakin ciki da damuwa wahala ce.
🏽Manta alheri butulci ne.
🏽Kafin ka roki Allah abin da ba ka da shi, ka fara gode ma sa a kan abin da kake dashi, don shi ne ya ba ka.
Barkammu da Safiya