TA'AZIYYAR DILIP KUMAR
Da sunan Allah na mai girma
Wannan da ya yo mu mai rahama
A wurinsa gafara muke nema
Mun yarda da kai babu tantama.
Tsira da aminci mai girma
Ga manzon mu mai girma
Wannan da muke yi wa hidima
Duk ya so ba shi nadama.
Kwana dai in har ya ƙare
Tafiya ba wanda zai kare
Ba 'ya'ya ba matan aure
Hakanan ran ka za fa a zare.
Ko ka yo aikin alheri
Ko kuma ka yo na sharri
Hakanan za a saka cikin kabari
Wannan shi ne batu na zahiri.
Dilipu Allah ya jiƙanka
Ya gafarta maka laifinka
Ya shafe maka zunubanka
Ya ƙaro haƙuri ga iyalanka.
Allahu ya sa mutuwa ta zamo hutu
Na cutuka da suka yi katutu
Ya zamo tafiya ta zama hutu
Kowa tabbas ai za ya mutu.
Allah muna roƙo ka yo rahama
Ga bawan nan naka mai himma
Ka sa ya ruwan ƙorama
Ƙoramar tafki na rahama.
Saura mu ma muna kan hanya
Allahu gare mu ka yo shiriya
Mu zamo mun zauna kan hanya
Mu daina faɗa ko jayayya.
In lokaci yayi cikin sa'a
Mu tafi muna a cikin sa'a
Bakin mu da sunan Allah na
Da abin sona manzona.
Haimana ne yake yin baiti
Baitin batu da ke kan saiti
Saitin da san ya fi na titi
Allah tsare mu da yawo kan titi.
©️✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Haimanraees@gmail.com