MAGANIN ZAFIN KISHI

*MAGANIN ZAFIN KISHI ! !*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
DON ALLAH MALAM MENENE YAKE KAWO MATSALOLI TSAKANIN KISHIYOYI, SABODA INA SON NA KARA AURE ?
*AMSA*
Wa'alaykumussalam,
To malam Kishi wata dabi'a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A'isha tana cewa : "Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta" Bukhari 1388
Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, za mu iya mayar da abubuwan da suke kawo kishi mara tsafta zuwa abubuwa guda hudu, wadanda in har da za su warwaru, to da ka ji dadin zama da matanka, saboda za su zama kamar 'yan biyu :
1. Jahilci : ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar : rage yawan zawarawa da 'yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi s.a.w., domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu.
2. Mummunan zato, yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.
Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba'a samu matsala ba.
2. Rashin adalci daga wajen namiji, yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba.
Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne : babu yadda za'a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi s.a.w. ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A'isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan kirdadi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne : rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.
3. Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.
IDAN HAR WADANNAN MATSALOLIN ZA SU WARWARE, INA GANIN ZA'A SAMU KISHI MAI TSAFTA.
Allah ne mafi sani
*Dr Jamilu Yusuf Zarewa*
2/9/2014
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH**HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA ?*
*Tambaya
Assalamu alaikum.malam wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin
*Amsa
Walaikum assalam To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi" Tirmizi ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :
1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba. Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.
2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3\567 sannan ita ce maganar Shafi'iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154
Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir shafi na : 481
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
15/8/2014

Post a Comment (0)