MENENE HUKUNCIN A CUCI MAZA?

Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,803:
=
Irin daurin dankwalin da akeyi yanzu da ake cema acuci maza, shin shima ya shiga cikin wadanda aka siffanta da kansu kamar tozon raqumi???
=
=
Amsa
=
=
Aa shi wannan daurin dankwali ado ne kawai kuma kwalliyace, wanda Allah ta'ala yace wanene zai hana kayan ado wanda Allah ya fitar dashi domin bayinsa...
     Amma dai bayyanashi mace tasa wannan dan kwalin kuma tariqa bayyanashi agaban wadanda ba muharramantaba wannan shine haramun amma babu laifi mace ta daura abinta acikin gida daga ita sai 'ya'yanta da mijinta ko muharramanta wannan babu laifi
     Amma lallai akwai wasu daga cikin malamai wadanda suke lissafa wannan dankwalin cewa ya shiga cikin wanda hadisin can yake magana na masu kama da tozon raqumi amma gaskya basuda wata qwaqqwarar hujja akan hakan. Dan haka lallai wannan dankwalin babu hujjar cewa kai tsaye shine ake maganarshi a wancan hadisin. Amma babu shakka sunanda ake kiran dankwalin dashi tabbas wannan sunan bai dace da ruhin shari'ar musulinciba cewa da akeyi acuci maza, domin ita shari'ar musulinci anginata ne akan LÃ DARRA WALÃ DIRARA wato Babu cuta kuma babu cutarwa, ADDURARU  YUZAL
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
مجلس تعليم الكتاب والسنة
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika

1 Comments

Post a Comment