BA'A YIN GATSE A SAKI !!!
Tambaya
Assalamu Alaiku Tambaya: Dr, mutum ne sukayi fada da kawun matarshi sai kawun matar ya ce dashi iyakaci dai kace ka saki 'yata, sai shi kuma mijin yace na saketa saki uku, amma matar ba ta gurin ma'ana ba ta jiba, sai daga baya ta samu labari, don Allah Dr. Menene matsayin Aurensu? Nagode Allah ya karawa Dr. Lafiya da Imani.
Amsa
Wa alaikum assalam, ta saku mana tun da ba'a wasa a saki, mutukar an furta ai kalmar ta zartu
Ba sharadi ba ne ayi saki a gaban mace, sannan take sakuwa, saboda yardarta ba sharadi ba ne.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
14/12/2016