RANCEN AIRTIME DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM?

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM?

```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM```

Na karanta rubutun da dan uwa Shehun Malami Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi akan wannan lamari kuma har na yi sharing tare da dan ta'aliki a kai. Na so na wadatu da wannan, amma sai na ga a wasu shafukan yan uwa ana ta tafka muhawara da sa bakin masu masaniya a Fikihu da wadanda ma ba su da ita sam.

Akwai masu ra'ayin cewa, an dulmuyar da Dr. Sani ne har ya canja fatawa. Ina son in fada ma wadannan cewa, sun jahilci wane ne Dr. Sani a kaifin basirarsa da bincikensa na ilimi. Ba na maganar wani dan bokon da bai san kimar ilimin annabawa ba don ya ce masa "Dan Arabiyya zalla" ko "Mai ido daya" . Domin ko ya sani ko bai sani ba da annabin Allah yake. Shi ne mai Arabiyya zalla. Kuma idonsa mai tsarki da tarin albarka bai taba kallon wani bokon da shi wannan jahilin yake takama da shi ba.

Littafin Allah da ya zo da shi Arabiyya ce zalla, haka ma hadisansa Arabiyya ne zalla. Ashe wanda ya sha su ya koshi shi ke zama dan Arabiyya zalla. Mai sukar sa ta wannan fuska kuma ya san ko waye yake suka. Allah ya shirye mu.

A nan dai ina son ne in dan kara haske a kan matsalar don masu neman bayani tsakani da Allah ko za su gane:

1. Riba tana shiga a cikin Bashi idan ya kasance kudi da kudi ne, aka samu fifiko saboda jinkiri. Misali, Zan ranta maka N1000 a karshen wata ka ba ni N1100. Wannan haram ne.

2. Hukuncin ba haka yake ba idan cinikin kaya ne. Misali, mai biredi a unguwarku tana sayar da shi a N180 amma duk wanda zai karba Bashi N200 za ta rubuta masa a karshen wata ya biya. Wannan ya halalta bisa ingantacciyar magana.

Lallai kam Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya haramta ciniki biyu cikin daya, amma wannan ba shi ne ba. Ciniki biyu ne daban daban. Farashin kudi hannu daban, na Bashi daban. Don haka ya halalta.

Karin bayani kan wannan a duba: Nailul Audar na Imam As-Shaukani.

3. A Fikihun musulunci ba a la'akari da sunaye. Ana la'akari ne kawai da ma'anoni. Kiran Riba da sunan interest ko service charge ko COT ko ma mene ne bai canja mata hukunci. Haka shi ma Bashi bai canja hukunci duk sunan da aka ba shi.

4. Mu koma kan waccan matar mai biredi idan aka kaddara tana sayar da recharge card. Shi ma ya halalta in saya a matsayin Bashi in kara kudi a lokacin biya. Sai in tafi gida da biredina da katina. Ni kuma a ranar biya na san akwai karin da zan yi don ba farashinmu daya da mai kudi cash ba.

5. Idan zan sayi kati a unguwarmu inyi kari don na karbe shi Bashi, don me ba zan saya ga kamfani ba?

6. Kenan airtime haja ce da ake saya don amfaninta ba kudi ce ba. Amma ana rubuta mata kimar kudinta a jiki kamar yadda ake lika kudin biscuits a jikinsa a supermarket. Kuma ya halalta mai supermarket ya ba da shi Bashi tare da karin kudi. Haka shi ma mai shago ko kamfanin MTN, GLO dss.

Mun tattauna wannan matsala a wani zama da muka yi a Abuja (March/April 2015) tare da:

🕯 DR. BASHIR ALI
🕯 DR. ABUBAKAR SANI BIRNIN KUDU
🕯 DR. MUHAMMAD SULAIMAN JOS
🕯 DR. IBRAHIM JALO JALINGO
🕯 SHEIKH MUKHTAR ABDULLAHI WALIN GWANDU (LIMAMIN CENTRAL MOSQUE NA BIRNIN KEBBI)

Dukkanmu mun cimma matsaya a kan halascin wannan ciniki bayan bahasi mai yawa na awoyi masu dama. A lokacin mun samu labarin cewa, Dr. Sani yana fatawa a kan haramcin sa. Alhamdu Iillah yanzu Dr. ya sake nazarin fatawarsa. Ba illa ba ne idan wani ya ankarar da shi nan take ya gane.

Ina kara jaddada kiran da Dr. Sani ya yi cewa lamarin Shari'a ba kowa ne zai tsoma bakinsa ba. Wanda bai sani ba yana iya yin tambaya amma kada ya yi jayayya ballai sakin maganganu na rashin ladabi ga magadan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Allah ya yi mana muwafaka.

Dan uwanku
✍🏼 Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
4 ga Shawwal 1437H (9/7/2016)

Gabatarwa: Abu-Unaisa.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)