*_IDAN UBA BAI YIWA DANSA YANKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA?_*
*Tamabaya*
Assalamu alaikum. yaa shaikh mutun ne Allah ta'ala ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi???
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.
Duk wanda bai samu damar yiwa dansa yanka ba a kwanakin da aka ambata a sama, to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi duk lokacin da ya samu dama.
AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa a lokacin da Annabi S. a. w ya ambata, wato ranar bakwai ga haihuwa, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha 1/615.
26/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.