Tambaya ta (295
:
Shin Ko Ya halatta Musulmi yakarbi abincin Kirsimeti yaci?
:
AMSA
:
Alal-Haƙiƙa ansamu Saɓanin Malamai dangane da hukuncin Musulmi yaci abincin da Ahlul-Kitabi (yahudawa da kiristoci) sukayi dan saboda murnar wani biki daga cikin bukukuwansu kamar Misalin irin bikin *Kirsimeti,* wato Asalidai ya halatta idan Kafiri yabawa *Musulmi* kyauta yakarɓa, domin hakan na'iya janyo hankalinsa ya sanyashi yaji yana *sha'awar Musluncin,* kamar yadda aka ruwaito cewa *Mαɳzσɳ Aʅʅαԋ(ﷺ)* yana karɓar kyautar da kafirai suka bashi, hakanan *Asali* ya halatta *Musulmi* yabawa *Kafiri* kyauta Musamman ma danufin janyo hankalinsa zuwa ga *Muslunci,* amma bai halattaba *Musulmi* yabawa *Kafiri* wata kyauta aranar *Idinsu (kafirai)* ko buku-kuwansu, domin yinhakan kamar yayi taimakekeniyane akan shirkar dasukeyi, hakanan baya halatta ga *Musulmi yabawa Ɗan-Uwansa Musulmi* wata kyauta aranar da *Kafirai suke Idinsu (bukukuwansu)* idan yabashine da nufin taya *Kafirai Murna* awannan ranar dakuma girmama wannan bikin dasukeyi, hakanan baya halatta ga *Musulmi* yasayarwa da *Kafirai* dukkan wani abinda zasuyi amfani dashi awajen bautarsu,_
:
_To Saidai *Malamai sunyi Saɓani* game da kyautar da *Kafiri zeyiwa Musulmi* aranar wani *Biki daga cikin Buku-kuwansu kamar ranar kirsimet,* wasu daga cikin *Malamai* sukace babu laifi *Musulmi* yakarɓi kyautar da *Kafiri* yayimasa aranar *Kirsimeti* amma da sharadin yakasance abinda akayi kyautar dashi dama asali halal ne awajen *Musulmi* yayi amfani dashi, sukace karɓarsa bata nufin cewa ya yarda da abinda sukeyi, hakanan kuma karɓar kyautarsu bata nufin antemakesu akan Shirkarsuba, Saidai abinlura anan shine, *Malaman* dasukace yahalatta akarɓi kyautar *Kirsimet* to suna maganane akan abinda ba yanka bane, wato suna maganane akan kamar abincin dasuka dafa ko *'Ya'yan itatuwa* ko makaman tansu, amma idan sukayi yanka wata Dabba danufin *Bikin Idinsu (kirsimet)* to bai halatta *Musulmi* yaciba, duk dacewa asali a *Shari'ance* ya halatta aci Yankansu kuma a auri *Matansu,* to amma anan yazama haramunne saboda sunyi yankanne da nufin wannan bikin nasu,_
:
_Saidai kuma agefe ɗaya akwai *Malaman* da sukace haramunne *Musulmi* yakarɓi dukkan wata kyauta da wani *Kafiri* zaibashi aranar idinsu *(kirsimet),* kuma koda menene indai anyishine ko antanadeshi saboda wannan rana ta *Kirsimet* to bai halatta yakarɓaba, waɗannan *Malamai* sukace idan *Musulmi* yakarɓi kyautar *Kafiri* aranar Idinsa, to kamar yayi taimakekeniya da aikin ɓarnane, Sannan kuma girmamawace agaresu da Ƙarfafarsu akan suci gaba dayi dakuma tayasu murna da farinciki akan ɓarnarsu,_
*(وَالـلَّـهُ سُـبْـحَـانَـهُ=وَتـَعَــالـَيٰ أَعْـلَـمُ)*
:
*_Doмυn nЄMan Ƙarin bayani sai aduba waɗannan Լitattafai kaMar Ӈaka:_*
*_↓↓↓_*
:
*"إقتضاء الصراط المستقيم" (1/251)*
:
*"التاج والإكليل" (4/319)*
:
*"تبين الحقائق" (6/228)*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
🇷 🇺🇧🇺🇹🇦 🇼🇦
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
*_Domin sђiﻮa sђaŦinmu daкє Ŧaςєbooк sai asђiﻮa wannan linк кawai aאi ""liкє""👇🏾_*
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi