*SANA'A DA WUTAR LANTARKI A GIDAJAN GWAMNATI ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam. Tare da fatan Allah Ya karbi ibadun mu da ku Alhazai baki daya.
Malam ina hukunchin wanda suke zaune a gidan hukuma, kudin wuta da ruwa duk hukuma ke biya. Ya halatta suyi harkan kasuwanchi da ruwa da wuta, kamar niqa gari, ko yin qanqara suna chin kudin da suka samu. Ina matsayin wannan a Shari'a?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, In har a cikin albashinsa ake dauka babu laifi in ya yi sana'a kamar yadda hakan yake faruwa a cikin albashinmu na malaman jami'o'i, tun da hakkinsa ne kuma in da ba ya shan wutar da ba'a cira a albashinsa.
Misali a A. B. U. Zaria hukuma tana cirar min dubunanai daga Albashina duk wata, saboda wutar lantarkin GIDANA, kin ga babu laifi in na yi Sana'a da wutar saboda na riga na biya.
Amma idan akwai sharadin da hukuma ta sanya na hana amfani da wutar a wasu halaye da kuma lokuta ko wasu kayan lantarki saboda kar asha ta wuce ka'ida ko gudun fadawa hadari ya wajaba a kula da su, mutukar bai sabawa sharia ba, tun da musulamai suna kan sharudansu ne kamar yadda hadisi ya tabbatar .
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
28/08/2017
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi