Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,783
=
Game da suna humaira naji wasu nacewa bakyau kuma sunan ya'ta Aishatu ne akece mata humaira to wai da gaske ne
=
=
Amsa
=
=
Toh Humaira ma'anarta shine 'Yar Ja, wanda asali daga Hamra'u ne, wato Ja, se akayi tasgirinsa ake cewa Humaira, wannan kuma wani salo ne na larabawa idan sunaso su qanqanta abu, ga babba ga qarami ga kuma dan qarami toh wannan dan qaramin shine suke tsamo sunanshi daga jikin sunan babban, misali Umar, idan kanaso kace dan qaramin Umar sekace Umair, Usman idan kanaso kace dan qaramin Usman sekace Usaimin, Salaha idan kanaso kace 'yar qaramar salaha sai kace Sulaihat, Zaliha kuma Zulaihat, toh itama Humaira asali daga Hamra'u ne wato Ja, idan kanaso kace 'yar Ja wato qaramar Ja shine sai kace Humaira, kuma wannan sunan babu laifi acikinshi domin ko acikin hausawa akwai wacce ake cemata 'yar ja kuma tana amsawa, toh ma'anar wannan 'yar ja din shine Humaira.
Amma Aisha tasamu laqabin Humaira ne daga Bakin Annabi (s.a.w) lokacinda Aisha tatare a gidan Manzon Allah to 'yarsa Fateema ta girmi Aisha, ita kuma Aisha tana ganin kanta matsayin matar uba gakuma quruciyarda take kansu a wannan lokacin se suka riqa dan samun sabani tsakaninsu toh shikuma Annabi (s.a.w) kokadan bayaso a ta6a masa Fateema duk da cewa tafi qarfin Aisha amma sai Annabi (s.a.w) yake gayanata ke 'yar ja (Humaira) ki kiyayi fateema, toh daga bakin Annabi (s.a.w) aka samo wannan laqabin na Humaira kuma matarsa Aisha yake gayama haka kasantuwarta Ja ce kuma yarinya qarama a wancan lokacin, to daga nan aka samo kiran duk wata me suna Aisha da wannan laqabi na Humaira, kuma babu Yadda Za'ayi Annabi (s.a.w) ya sanyawa matarsa laqabi wanda ba me kyauba, dan haka babu wani laifi dan ancewa Aisha Humaira Insha Allahu
=
=
Allah yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
مجلس تعليم الكتاب والسنة
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika