MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMIN SA DA GANGAN?

*_MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN!!_*

                              *Tambaya:*
Aslm Na wayi gari da azumi sai aka kawo abinci sai na fasa azumin naci abincin, malam yin hakan akwai laifi na sharia?

                                  *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, ya halatta abin da ka yi, saboda fadin Annabi (S.A.W) "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya so ya cigaba da azumi, in ya so kuma ya karya". Kamar yadda Tirmizi ya rawaito

Allah ne mafi sani.

25/7/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)