MATA ZASU IYA YIN SALLAR JANAZA?

*_MATA ZA SU IYA YIN SALLAR JANA'IZA?_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum, malam ya halatta mata subi sallar jana'iza? saboda na ga wani malami lokacin da aka kashe masa yaya har mata ya tara aka yi musu sallar jana'ixa Ngd malam

                                 *Amsa*
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa ya halatta mata su yi sallar jana'iza, saboda dalilan da suka zo akan sallar jana'iza ba su banbance tsakani mace da namiji ba.

Duk nassin da ya zo daga Al'qur'ani ko sunna, to yana hade maza da mata wajan hukunci, in ba'a samu wani dalili ko alama wacce ta fitar da su daga ciki ba.

Sannan mata sahabbai sun yiwa Annabi S.A.W sallah bayan ya mutu, babu kuma wanda ya yi inkarin hakan, sai wannan ya nuna shi ne shari'a.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)