*_ZAN IYA AURAN JIKAR YAYATA?_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, Allah yasa Malam yana cikin koshin lafiya. Malam Ina neman a warware mun wata matsala ne, Akwai aure tsakanina da jikar yayata? Wato dani da kakar yarinyan mahaifinmu daya.
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, Babu aure a tsakaninku mutukar mahaifiyarku daya da kakarta, saboda aya ta (23) a suratun Nisa'i ta haramta auran 'yar 'yar'uwa wacce kuke uwa daya ko uba daya ko kuma shakikai.
'Yar 'yar'uwa a wannan ayar ta hada da Jikarta da jikar jikarta har zuwa can kasa kamar yadda malaman Fiqhu su ka yi karin bayani.
Don neman karin bayani duba babun NIKAH a Fiqhul Muyassar da tafsiran malamai ga aya ta (23) a Suratun Nisa'i.
Allah ne mafi Sani.
19/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.