*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_KI YI ADO DA KWALLIYA SABODA MIJIN KI_*
Ki kasan ce kamar wata kyakyawar fulawa ma abociyar kyau da daukar hankali tare da kyakyawan kanshi ga mijin ki
Ki fuskance shi da mafi dadin kamshi da mafi kyawun tufafi
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:
“Mumini bai amfana da komai ba bayan kiyaye dokokin ubangiji mafi alkhairi gare shi sama da mace ta gari, idan ya kalle ta zata faranta masa rai”
Nana Aisha ta ce: mata ku kwadaitu da yin kwalliya ga mazajen ku
Idan kina da miji kike so kiyi masa magana toh kiyi ta a mafi kyawun yadda take
Umamatu bintul Haris tana yiwa yar ta nasiha yayin auren ta tace:
Kar idon sa ya ga mummunan abu daga gare ki
Kar hanchin sa yaji kanshi daga gare ki sai mafi dadi
Abdullahi bn Ja’afar yana yiwa yar sa nasiha yayin auren ta
Kwalliya ta zama dole a gare ki
Ki sani kuma hakika mafi kyawun kwalliya shine kwalli
Kuma mafi kyawun turare shine ruwa (yana nufin ki sance mai yin wanka a koda yaushe, saboda idan babu wanka toh kwalliya da turare basu da amfani)
Wata mahaifiya tana fadawa yar ta a lokachin auren ta
Kar ki yarda ki bar yin kwalliya
Sai yar ta ta ta kasan ce tana yiwa mijin ta kwalliya har ta wuce shekara 70 a rayuwar ta
An tambayi wani mai hikima akan wacece kyakyawar mace
Sai yace:
Itace wacce take samun damar isuwa ga idon mijin ta da hanchin sa da zuciyar sa
Asma bn Kharija alfaza’riy ya aurar da yar sa
Yayin da zai mika ta ga mijin ta, sai yace da ita:
Kar ya ji shin shi ni komai daga gare ki sai mai kyau
Kar yaga komai sai mai kyau.
Yar uwa ta musulma Ko kina kwalliya domin mai gidan ki Shugaban ki Jagoran ki
Ko kuma ballagaza ce ke kazama a cikin gidan ki
Ba kya yin kwalliya da ado sai zaki biki da unguwa ko kasuwa ko asibiti
Ya kamata mu gyara domin mu samu cikakken cigaba a cikin gidajen mu.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*