MU JI TSORON ALLAAH

MUJI TSORON ALLAH

((TAKAWA)) "Hattara 'Yan Mata Wajen Aikata Alfsha da Sunan Shan Minti" (1)

Fitowa Na 017

Takawa; Takawa shine jin Tsoron Allah a duk inda rayuwar Musulmin kwarai ya kasance, wannan Shi ake kira Takawa, ya ke Yar Uwa na Musulma, kada misali kina a matsayin ki na Musulma, kinada Martaban ki da Kimar ki da Dajarar ki mai tarin Girma da Kimar ki da Mutuncin ki a wajen Allah mai Girma da daukaka, da ma wajen wanda su kasan Allah da Manzon Allah, ki tsaya ki wasar da kanki ko wanne filawa ya samu nashi ruwan. 
      Idan kina cikin gidan ku ga tsoron Allah kamar yaya har ma zaki iya yiwa wasu yan Uwanki Nasihar kada suyi abu kaza da abu kaza, domin yin Shi Haramun ne babba, amma da zaran kin bar cikin gidan ku, kin fita waje duk wannan Tsoron Allah'n da Nasihar ki duk kin bar su a cikin gidan ku, yanzu kin fita waje babu Kalan Alfashan da ke baki aikatawa, har kin addabi Jama'ar gafen wasu Unguwan, inda wani ko wata wanda ta san ki ta san komai naki inda zata ganki a wannan halin, sai ta tsaya tanata mamakin ki, domin ke ne kike yin Nasiha Allah yace abu kaza Haramun ne, amma gashi idan kin fita waje inda wasu yan unguwan ko mutanen gidan ku basu iya ganin ki, kin zo kina aikata abubuwa dabam dabam iya son ranki, to idan mutanen unguwan ku ba ganki ba, to Mala'ikun Allah sun gani kuma sun rubata, sai mu ga da ganin Mala'ikun Allah da na mutane wanne zai fi tasiri a ranan Alkiyama, 
      Ko kuma Misalin ke Matar Aure ce, in kin fita waje ga ki kinan Mumuna ga kalmar Allah a bakin ki kamar na Manyan Malamai, amma kuma kina sa kafar ki, idan kin dawo cikin gidan ki, to wannan Tsoron Allah'n da kike nunawa Jama'a a waje, duk kin bar su a can, yanzu kin dawo gidan ki duk kin fitini kowa yaran ki ma ba ki bar su ba, Mijin ki ma baki Bar Shi ba, kowa kin addabe shi wajen furta musu Kalmar da Shari'a bai yadda da shi ba, ko kuma ke a gidan ki kina nunawa Mijin ki ga Tsoron Allah'n ki a fili, amma kina fita waje kindawo Shu'uma kenan komai kina iya aikatawa ko a jikin ki. 

To a zahirin gaskiya, ba shi ake kira Takawa ba, an Tambayi Umar Allah yakara yarda gare shi, shin menene Takawa? Yace Misalin Takawa shine kina cikin Tafiya cikin dokar Dajin da yake da 'Kayoyi cikinta, kuma gashi Kafar ki babu Takalmi, to yaya zaki yi Tafiyar a wannan lokacin? 
       Ai a Lokacin sai kin tsaya sib, kin daidaita Sahu sosai hankalin ki ya tattaru waje guda, kin duba dakyau ina ne babu 'kayan nan, wajen ne kafar ki na farko zai fara sauka, sai ki sake dubuwa ina ne inda babu 'kayan sai ki sake ajiye dayan kafar ki, a haka ne zaki yi tayi har ki fita daga cikin wannan Dajin ba tare da wani 'Kaya ya tsoke ki ba, Umar yace wannan shine Misalin TAKAWA, 
 
Duk abinda Allah da Manzon Allah ki kaji ance ko kika karanta cewa lallai an yi Hani akai cewa aikata shi Haramun ne ga hukuncin shi, to sai Takawar ki ya sa ki ki guji wannan abun, Misalin yin Zina Haramun ne, to karma ashe kin kusan ce shi koda wasa, kusantar Zina shine yawan Kalamai na Batsa, yawan kallon hotuna wanda suke sirara ne, kollon videos na Batsa, Rungumar Namiji a matsayin ki Na Mace Musulma ta ko wanne fanni ne, Taba Jikin Namiji wanda shi ba Muharramin ki bane, yanzu harda Shan Minti ake yi, idan ma ke bakiyi Namiji zai ce baki waye ba, ko kuma kawar ki ta addabe ki cewa kai ya waye amma ke har yanzu baki waye ba, 
       Ina wayewa ana nan bayan kin sabawa Allah da Manzon Allah, ai babu Jahilcin da ya wuce wannan, gara ma ita da batayi sau dubu Dari taki wayewa nesa ba kusa ba, kuma kina mutuwa a wannan halin idan baki tuba kika daina ba, babu abinda zai hana daga Kabarin ki baki ga Azaban Allah Kala Kala ba, ai Shan Mintin ma a wajen wasu ke baki iya ba, kenan haka zakiyi ta ganin azaban Allah Kala Kala kamar yadda wata ko wani zai ce miki ai baki iya ba a sake chanja wani Kala, haka Mala'ikun Allah zasu yi ta chanja miki wani Kala Azaban har Ranan tashin Alkiyama,
       Wallahi kimar ki na Diya Mace Musulma wallahi ya wuce ki tsaya da Saurayi ba Auren ki yayi ba, ki tsaya ki bashi ko da tafin Hannun ki ne ya taba, Kimar ki ya wuce haka, wallahi 'Yan Mata kuyi Hattara kasani cewa Zaku mutu, sannan kisani cewa Zakiyi Aure nan gaba, Namiji mai Mutunci barai taba tsayawa yace zai yi irin wadannan abubuwan dake ba, duk wanda yace zai taba Jikin ki ko zai rungume ki ko zai yi Shan Mintin da ke, da suna Lallai shi yana son ki ne yana kaunar ki, yace miki ai yin hakan shine zai kara tabbatar miki da cewa ai yana kaunar ki, to ki Tambaye shi kiji, shin idan Kawan shi ne ko Kuma Misalin ace Diyar shi ne, Wani Namiji ya zo zai yi mata irin haka zai yadda ya bar su? Ki tamabaye shi haka, idan Yace Eh, kema kin san sauran, idan yace A'a kin san wani mataki yake a wajen ki, ya ku 'Yan Uwa na Mata kuyi Hattara a daina yaudaran ku da kalmar so da kauna, alhalin ba haka yake a cikin zukatan su ba, kawai suna neman wani biyan bukatan su ne, kuma da sun biya bukatan su shikenan sun bar ki babu yadda kika iya kuma, 
    ana shin zarafin ku da sunan ana son ku, ku kuma kuna yadda da abinda ake furta muku, baraki taba gane cewa lallai abinda kike yi ba daidai bane sai Lokacin da kika yi Aure kika Haihu, 
      Saboda haka, kin ji An ce Miki shan Giya ko kuma shan Wani Kayan Maye wanda zai gusar miki da hankalin ki a Lokacin guda Haramun ne, to duk wadannan abubuwan, sai Takawar ki ya sa ki, ki ki jinin wannan abun, 

Zalunci babu kyau, yin Gulma ko shaidar Zur Haramun ne, sai Takawar ki ya sa ki ki guji wannan, zuwa Fati ko Kauyawa Dance da dai Sauran su, Haramun ne tunda bawai ana cewa Allah yace Annabi yace a wajen ba, sai Takawar ki ya hanaki zuwa irin wadannan wuraren, kallon Batsa ko maganar Batsa Haramun ne, sai Takawar ki ya hanaki aikata su, sauraron wakoki Haramun ne, idan bawai na yabon Annabi bane, sai Takawar ki ya hanaki, 
        Idan har kin dauki Kafar ki kin bar cikin gidan ku to sai inda Allah yace Takawar ki yasa ki haka, idan kina yin magana a kullum ke bakin ki baya fadan abinda Shari'a bai yadda da shi ba, Takawar ki ya saka ki yin haka, abinda Allah yayi Hani ki hanu baki yin shi saboda Tsoron Allah, kada kiyi Allah ya kama ki a Ranan Alkiyama da laifin kin aikata abu kaza saboda yau azaba ya tabbata a kanki, kuma ke abinda Allah yace ayi kina yin shi akan lokacin sa kamar yadda Annabi yace ayi, ke baki Sakaci wajen yin shi saidai inda karfin ki bai je ba, da dai Sauran su, idan kin kasance a haka, to kinada Takawar ki, kuma indai kin tsaya a wannan hali naki, har Allah ya dauki Ranki da kina jin Tsoron shi, shiyasa kike bin duk wani hani da yayi, ki ga kin kare kanki daga aikatawa, to kin huta__________

Ku Biyo Mu a Fitowa Na Gaba in Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zai Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar haka 
08164223447. 
This Is Only For woman Please.


Post a Comment (0)