SIRRIN ƁOYE
Rubutacciyar waƙar sirrin ɓoye, daga bakin Aminu Ala.
Bari bari zubar da hawaye
Don kuwa na ga sirrin ɓoye
Bari bari zubar da hawaye
Don kuwa na ga sirrin ɓoye.
Hmmmmm
Bari bari zubar da hawaye
Don kuwa na ga sirrin ɓoye
Muƙallibul ƙulubu buwaye
Iza aratu koma meye
Kun fa ya kunu ba tawaye
Da ka faɗa a take a waye
Za a ga ta kasantu buwaye
Ƙarfa ta ainu ta fi tsumaye
Ga ni tsaye bisan sawaye
Na tsayuwar da ba tawaye
Na durƙusa bisan gwiwaye
Nai sujadar da ba tawaye.
Masa bugun gaba a yi maye
Me sa a zam kamar ɗan yaye
Ka yi kama da me shaye-shaye
Kana watangaririya waye
Ba shi gwani ko ɗan waye
Saka maza da mata maye
Sanya ƙulafuci ya na maye
Bari bari zubar da hawaye
Cikin ido ake tsawurye
Don kuwa na ga sirrin ɓoye.
Na yi gamo da yaban tsoro
Nai kaciɓus gamon ban tsoro
Na ga abin da ya zama horo
Ga ni a kwance sai dai roro
Murƙususu nake don horo
Ga ko tsumaye me yin sharo
Na ji da ka a zuci na tsoro
Na ga hawaye na ta ziraro
Ɗaga ido da ya ban tsoro
Don kuwa na ga sirrin tsoro.
Abin da na gani da idona
Ya sarayar da dukka haƙona
Nai ru'uya da sirrin ƙauna
Hoto na zuci ga shi a baina
Abin da ke cikin ƙalbina
Shi zahirin ido zai nuna
Abin da ke cikin ruhina
Ga shi ƙiri muzu fa da rana
Kun ji abin da ya kaɗa raina
Na yi ƙuru-ƙuru da idona.