FALALAR AYOYI, MAGANI, WARAKA DAGA AYOYIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. DAGA BAKIN DA BAYA KARYA RASULULLAHI S.A.W.

FALALAR AYOYI, MAGANI, WARAKA DAGA AYOYIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. DAGA BAKIN DA BAYA KARYA RASULULLAHI S.A.W.
      Ya ku 'yan uwa maza da mata ga falalar alqurani ko ma bayan bokayi 'yan tsubbu da 'yan bori. Wanda duk ya riki wannan hanya hakika ya rike igiya wadda bata tsinkewa sannan babu nadama babu kokonto ga wanda ya rike alqur'ani ya zama magani na cutuka na jiki da na zuciya. Ko bakin ciki ko mummunan makoma.
       Ya ku 'yan uwa ku biyomu domin jin magani daga bakin da baya karya.
1)SURATUL FATIHA: Karanta suratul fatiha tana hana fushin Allah, wato Allah ya yi fushi da kai saboda mummunan ayyukanka.
2)SURATUR YASIN: Tana hana 'kishirwa ga masu karantata a ranar alkiyama. Karantata a kan wata bukata ka roki Allah da ita Allah zai biya maka bukatarka kowace iri ce. Sannan karantata ba tare da wata bukata ba za a baka ladar sabke alkur'ani sau goma.
3)SURATUL WA'KI'A:(IZA WA'KA). Tana hana talauci duniya da lahira
4) SURATUL MULK: Tana hana azabar kabari
5)SURATUL KAUSAR( INNA A'ADAINA): Tana hana husuma da jayayya.
6) SURATUL KAFIROON( QULYA): Yawan karantata na sa mutum ya cika da imani, tana hana shaidan cin galaba a kanka lokacin mutuwa
7)SURATUL IKLAS: Yawan karantata yana hana mutum munafinci ba za ka zama munafiki ba.
8)SURATUL FALAQ: Tana hana mutum hassada idn yana karantata koyaushe
9)SURATUL NAS: Idn mutum na karantata tana hana yawan waswasi
10) SURATUL DUKKAN: Yawan karantata koyaushe tana sa mutum ba zai sha wuya ba ranar alkiyama komai zai yi cikin sauki.
    Da fatan wannan sako zai amfani al'umma. Don Allah don girman Allah duk wanda ya same shi ya tura domin ya sami ladar sadakatul jariya
     Sannan ya ku 'yan uwana a musulinci kuskiren da ke ciki daga gareni ne sai a yi mani uzuri domin ni 'yar adam ce.

Post a Comment (0)