HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR HADDAR ALQUR'ANI

HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR HADDAR
ALQUR'ANI

1. Ka fara haddar ka da addu'ar
neman taimakon Allah cikin wannan niyya taka ta
alheri.
2 Ka kula sosai da kanka wajen nisantar
kazamtar haramun, wato ka tsaya wajen cin
halal, domin cin haram yana toshe basirar Dan
Adam
3. Ka nisanci fara hadda don burin samun
dukiya, kuma ka cire kwadayin abin duniya a
zuciyarka. Haddar Alqur'ani bata zama a cikin
kwakwalwar duk wanda ya matsu yaga ya tara
dukiya a cikin haddar sa da zafi-zafi.
4. Kayi
karatu a wajen Malami na Allah wanda yasan
Karatun, Kuma serious malami wanda ya maida
hankalinsa akan hidimtawa Alkur'anin.
5. Ka nemi
goyon bayan mahaifan ka tare da rokon
addu'arsu, don sanya albarka daga iyayenka
ginshiki ne wajen nasarar samun haddar ka cikin
sauki.
6. Kaifin basira da hazaqa yana taimakawa
wajen saurin samun yin hadda mai kwari cikin
karamin lokaci
7. Ka fara hadda da niyya mai
kyau, wato ka zamo mai kwadayin son karatun
da burin haddar alkur'ani.
8. Ka zamo mai juriya
akan kowacce irin wahalar da zaka riska a wajen
neman karatun ka, ka cire son hutu da yawan
kasala ko son nishadi da wargi da zai jawo maka
lalaci.
9. Tanadin abinci yana da muhimmanci
don ka samu natsuwa, don ba'a iya hadda mai
kyau da yunwa amma kar kace sai kaci mai kyau
kasha mai kyau a kullum.
10. Kar ka sanya
gaggawa wai sai ka gama hadda a karamin
lokaci, ka natsu ka bi a hankali domin ba'a
samun ilimi a cikin dare daya.
11. Samun abokan
karatu na kirki da zaku na tafiya tare cikin hadda
yana taimakawa, amma ka kiyaye Idan fa
abokanka suka zamo na banza, ko wadanda basa
son karatun ko masu kasala to tabbas ka hadu
da matsala da ci baya a harkar karatun ka.
12.
Ka tsara gwargwadon abinda zaka na haddacewa
a kullum, wato kamar ka tsara cewa a duk cikin
kwana 3 zaka yi haddar allonka ko shafi daya ko
biyu ko makamancin haka..
13. Ka rika karanta
wuraren da ka haddace a cikin Sallar ka ta farilla
da nafiloli a kowanne wuni.
14. Idan da dama ka
nemi allo ka rubuta da kanka wajen da kake son
ka haddace, ko ka samu littafi mai rubutun da
idon ka zai karanata sosai, sannan kayi ta
QwamI.. Ba-ji ba-gani.
15. Ka tsarawa kanka
lokaci a cikin safiya da maraice kana tilawa na
maimaita wurin karatun ka adadi mai yawa, wato
kana biyawa a kullum kamar sau 100 in zaka iya.
16. Ka za6i yin tilawa da dare da jijjifin safiya, ka
tsara yadda zaka Qaranta barcinka, kuma abinda
yafi shine kana bacci da wuri don ka samu tashi
cikin dare, ka kula wajen cin abinci madaidaici,
Ka takaita yawo da surutu maras amfani da
zaman wurin hira. kuma ka rage yawan abokai
17. Ka kula sosai da yawan ibada da nisantar
aiyukan sa6o.
18. Ka gujewa sauraron wakokin
banza da raye-raye da kallon film don suna
makantar da zuciya.
19. Ka tsare harshen ka
daga batsa da zagin mutane da kallon haramun
da latse-latsen waya maras amfani.
20. In kana
samun wahalar rike hadda kayi hakuri ka dogara
ga Allah, ka yi juriya ka nisanci debe tsammani
da karaya a zuciyar ka. Lallai in kana himma da
dagewa zaka samu taimakon Allah. Ina rokon
Allah ya karfafa niyyar mu, ya cika mana burin
mu ya hore mana saukin hadda ya bamu karatu
mai albarka.

Post a Comment (0)