HUKUNCIN SAKIN MAI HAILA

*_HUKUNCIN SAKIN MAI HAILA_*

                                   *Tambaya:*
Assalamu alaikum Malam mun samu rikici da matata ko ya halatta na sake tana haila??

                                       *Amsa:*
Wa'akaikum assalam Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin Allah "Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a farkon iddarsu) Suratu Addalak aya ta farko, wato a farkon tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba.
Ana nufin a halin da za su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin... tsarkin da bai take ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za'a kirga da ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya sadu da ita, domin bai sani ba shin ta dauki ciki ta yadda iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta dauka ba ta yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai sakin ya haramta.

Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa Annabi ﷺ labari, sai Annabi ﷺ ya yi fushi, sai ya ce "ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita"

*_ANA TOGACE GURARE GUDA HUDU WADANDA SAKIN MACE MAI HAILA YAKE HALLATA_*

A. Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya sabawa fadin Allah madaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba.

B. Idan ta yi hailar ne tana da ciki kamar yadda aka riga aka yi bayani a baya.

C. Idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL'I) to anan babu laifi ya sake ta tana haila.

D. Idan ya yiwa matarsa I'laa'i kuma aka yi watanni hudu bai  dawo ba.

Allah ne  mafi sani

21/2/2013

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)