*_BA YA HALATTA AYI SALLAH KAFIN LOKACINTA!!_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum Dr. ni student ce idan mukashiga lecture munakai kusan magariba bamufitoba to malam zamu iya jawo sallolin na hadasu kamar yadda matafiya keyi ?
*Amsa*
Wa'aleikum assalam, Ki yi iya kokarinki wajan yin sallah a lokacinta, saboda fadin Allah madaukaki "Allah ya wajabta sallah ga muminai a lokuta kayyadaddu" Suratun nisa'i aya ta:(102), ina har kika jinkirta salloli ba tare da uzuri ba kin sabawa Allah kuma a wajan wasu malaman Allah ba zai amsa ba in kika yi daga baya.
In har babu yadda za ki iya yin sallar a lokacinta Za ki jira har sai kun fito sai ki rama, saboda ba'a sallar farilla kafin lokacinta amma ya halatta ayi ta bayan lokacinta musamman in har da uzuri karbabbe a sharia.
Addinin musulunci ya togace sallar la'asar da Isha ga matafiyi saboda tafiya yankin wahala ne.
Allah ne mafi sani
22/02/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.