HUKUNCIN SHUGABA BAYA HALATTA HARAM

*_HUKUNCIN SHUGABA BA YA HALATTA HARAM !!!_*


                                *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam ga tambayata. mutum ne ya ya kasanche yana son yayi karatu, amma kuma bashi da ishesh shen kudi, sai yaji gashi ana tallafawa wanda suka riga suka fara karatun, dan akara musu karfin guiwa wajen himma da kwazo. wato (shucorlarship) sai ya kasance shi kuma yana da hanya wanda zai iya samun wannan kudi na (scolarship in) duk da dai bai fara karatum ba,kuma asali, ana bawa wanda suka soma ne.Toh mallam ya hallatta ya karba har indai karatun zai fara da wannan kudi. amma kuma kudin, ba na jaharsa bane, na wata jaha ce da ban, amma yana da wata hanya da zai iya samun wannan kudi .toh! YAHALLATTA YACI KOKO A'A MALAM?


                                    *Amsa*
Wa'alaikum assalam, To abin da zan iya cewa shi ne: ya ji tsoron Allah, ya bi ka'ida wajan amsar kudin, kada ya amshi kudin da a kundin tsarin mulki ko dokar shariar musulunci ba'a bawa irinsa. In har aka ba shi kudin da ba'a bawa irinsa, saboda yana da hanya ko kafa a wurin to ya ci haramun, yana dağa cikin ka'idojin musulunci : حكم القاضي لا يحل حراما ولا يحرم حلالا don haka ko da shugaba ya halatta maka kudin hukuma wanda baka cancance su ba, ba zai zama halal a wajan Allah ba, wannan sai ya wajabta yın taka-tsantsan.

Allah ne mafi Sani.

28\1\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (0703
6073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)