NASIHA CIKIN MUTANE TOZARTAWA NE

*_NASIHA A CIKIN MUTANE, TOZARTAWA NE!!!_*


                              *Tambaya:*
Asslamu Alaikum. Don Allah Mallam mene ne hukuncin wanda idan ya ga anyi kuskure yake tozarta mutum a cikin jama'a?! Shugaba ne na makaranta yake jan jam'i rana daya dalibi yaja da aka idar da sallah sai aka fara yiwa dalibin tozarta a gaban dalibai maza da mata kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kira shi gefe an masa nasiha da karin haske ko a hadasu iya maza ayi musu zai fi. Meye hukuncin haka?


                                  *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Yi wa mutum nasiha a cikin mutane bai dace ba, kuma hanya ce da za ta hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa nasihar yana da tsananin ikhlasi ba, Annabi (S.A.W) yana cewa: "Wanda ya suturta Musulmi Allah zai suturta shi". Kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2074.

 Allah ne mafi sani

20/11/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (0703
6073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)