IDAN MIJI YA YI LAYYA



*_ASSALAMU ALAIKUM_*
=
=
AMSOSHIN TAMBAYOYINKU
         
*DAGA ZAUREN
*📗ADDINI DA RAYUWAR DAN ADAM GROUP📗*
08186761010 ** 09038090522
:
.
_Tambaya ta (391)_
....
. _**_

_Assalamualaikum warahamatullahi wabarakatuhu,malam tambayata anan itace,idan miji yayi layya za'a raba musu ladanne shida matarda koko shi kadai za'a bawa ladar,
Koko dukda Allah yadurawa miji yima matarsa hidima, Amma idan akazo gurin layya bahaka bane dolene sai itama tayi tata da kanta idan tanada da hali koko ya abun yake ina neman karin bayani._
.
_
::
*_AMSA:-_*
_waalaikumussalamu Eh mana idan ya sanya matar itama zata samu ladan layyar Daman kuma ita layya Asali duk mijinda zai yi yana sanya matarsa ne cikin layyar koda su hudune duk babu laifi ya sanyasu cikin layyar kai bama iya matar ba dukkan iyalinsa zai sanyasu cikin layyar *Wannan shine Abinda ya tabbata cewa manzon Allah ﷺ yayi* Wato ya yanka raguna guda biyu *sai Yace daya shi da ahalinsa* dayan kuma *ga ďaukain al'ummarsa,* Hakanan suma sahabbai suka tabbata suna yi wato suna yin layya tare da sanya iyalinsu cikin layyar. Sabida haka idan mijin yana da halin siyama kowane daya daga cikin iyalinsa Abin layya to babu laifi yayi hakan, Idan kuma Rago daya yake da halin siya to sai ya sanya iyalinsa cikin layyar Kai idan ma bashi da halin yin layyar to yayi hakuri kada ya damu kansa domin shima ya shiga cikin mutanan da Manzon ﷺ yayiwa layyar hakanan suma iyalin nasa suma sun shiga. Sabida haka mata Abin ba na kallafawa mazanku bane cewa sai sunyi muku layya Idan basu da halin yi sai kuyi hakuri idan ku kuna da halin yi sai kuyi layyar_****
..
_Wallahu A'alam_

_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ_
_idan Anga Gyara A Sanar Damu  👏_
=
_Na So Kun San Tarin Lada Da Albarka Da Ake Samu Ta Hanyar Yada Ilimi  Ko Wani Alkhairi_
=
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu 

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)