SHEKARU NAWA ABU HURAIRA R.A YA LAZIMCI ANNABI S.A.W

*_SHEKARU NAWA ABU-HURAIRAH   (R.A) YA LAZIMCI ANNABI S.A.W?_*

                                  *Tambaya*
Assalamu alaikum
Mallam don Allah ina son in san shekara nawa aba hurera yayi a raye da manzon Allah,  kuma bayan rasuwar manzon Allah shekara nawa yasamu araye? Nagode malam. Muna musune da wani Dan shi'a

                                       *Amsa*
Wa'alaikumus Salam, To dan'uwa Abu-hurairah ya lazimci Annabi ﷺ tsawon shekaru uku, kamar yadda Bukhari ya rawaito a sahihinsa 1\359, sannan bayan Annabi ﷺ ya bar duniya ya yi shekaru 47 kafin ya rasu, don haka Abu-hurairah ya rasu a shekara ta 57 bayan hijra.

Wasu daga cikin malaman tarihin suna cewa: Abu-hurairah ya musulunta tun a shekara ta bakwai a watan Safar lokacin yakin Kaibar, don haka sai ya zama ya rayu a musulunci kafin Annabi ﷺ ya bar duniya, shekaru hudu da wata daya, sai a dauki abin da aka rawaito a Bukhari a matsayin gwargwadon lazimcitarsa ne shekaru uku, kamar yadda ibnu Hajar ya fada a Fathul-bary 6\608..

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Al-isaabah fi-tamyizissahaabah 7\444.

26\2\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)