DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 05

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN

Kashi Na É—aya 03

Fitowa Ta Biyar 05

Daga Haiman Khan Raees

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Barkan Mu da Warhaka.

A wanna fitowa kuma zan kawo muku wasu Zantuttuka ne na wannan Jarumi waɗanda su ke ƙunshe da saƙonni na soyayya, jan hankali da kuma Nasiha dangane da abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Mafi yawancin waɗannan zantuka ya furta su ne a wajen tarukkan sa aka gayyace shi. Ga su kamar haka:

1. “Kada ka zama masanin Falsafa kafin ka zama mai kuÉ—i". (har sai ka zama mai kuÉ—i)

 2. "Kada ku bari abubuwan da kuke tsoro su zama kwalayen da zasu rufe ku. Ku BuÉ—e su, ku ji su kuma ku maida su manyan abubuwan da zasu dinga Æ™arfafa muku guiwa. Na yi muku AlÆ™awari babu abinda zai É“aci". (idan kuka aikata hakan).

3."Ku yi karatu sosai, ku yi wasa Matuƙa. Kada ku bari wani abu ya dakatar da ku, kuma kada ku sake ku rayu a cikin mafarkin wani".

 4. "RuÉ—u wata hanya ce ta samun fahimta a duniya. Kada ka damu da shi sosai, kuma kada ka taÉ“a É—aukan kanka da muhimmanci ta yadda zaka yarda da Ra'ayin ka har ya kai matakin da zaka daina girmama Ra'ayin sauran Mutane".

5. “Nasara da rashin ta duk wani É“angare ne na Rayuwa, dukkan su suna zama ne na dindindin".

 6. "Ka bayar da wani abu naka zuwa ga mutane, kuma yayin da kake yin hakan, ka tabbata ka fahimci cewa ba wai kyautatawa wani kake yi ba. Komai KuÉ—in ka, komai Nasarar da ka samu ko É—aukakar da kayi, kada ka sake ka raina girman da jama'a suke baka kawai ta hanyar zaman su masu karÉ“ar kyautatawa daga gare ka".

7. "A duk lokacin da rayuwa ta yi maka ɗaurin minti, (ka sani cewa) ƙatuwar mota ba zata iya kwantar maka da hankali ba. Amma karamcin aboki yana iya yin hakan, kuma idan kaga baka samu nutsuwa irin wacce kake so ba, kada ka ruɗe. Komai na daidaituwa ne a hankali".

8. "Duk wani suna da zaka kira kanka da shi, ko wanda wasu ke kiran ka da shi matakai ne kawai. Ba da su ne za'a bayyana ka ba, komai kyawun su ko munin su. Abinda Ke bayyana haƙiƙanin ko kai wanene ita ce zuciyar ka".

9. "Duk iya aiki tuƙurun da za mu yi, Jagoranci ya nuna mana cewa dole mu tsammaci zuwan Masifa".

10. "Duk wani abu da ke maida kai baya ba zai Ƙyale ka ba har sai ka miƙe mishi tsaye ka fara saita hanyar ka da dukkan ƙarfin ka izuwa inda kake son zuwa. Don haka, ku bar Haniniya ku fara tafiya".

11. "Idan a karan farko baka yi nasara ba, yi sabon shiri sannan ka ƙara jarrabawa".

12. "Farinciki da baƙin ciki duk wasu ɓangarori ne na tabbatar rayuwa. Rayuwa tana tafiya daidai ne sakamakon canjin da ke wakana a tsakanin su. Kada ka ta'allaƙa kanka da ko ɗaya daga cikin su, domin a hankali kowannen su yana iya canzawa. Ka tafi da su tare kana mai yarda da cewa kowannen su zai zo ya wuce, ka yiwa kanka dariya idan kaga kana gab da Wargajewa, ka yi kuka idan kaga wani kafce na ya baka dariya".

13. “Nasara ba Malamar Æ™warai bace, rashin nasara ita ce".

14. "Ku rayu tun daga zuciya, ku yi soyayya, ku so mutane, ku so duniyar da take kewaye da ku, ku so dabbobi da Tsuntsaye, da manyan Birane da kuma tsaunuka, ku so Mafarkai, ku so rayuwa, ku so ayyukan ku, ku so abokan ku harda maƙiyan ku ma ko da kuwa ba da san ranku ba. Amma abu mafi muhimmanci abokai na, ku so kawunan ku".

15. "A duk lokacin da naji ina jin girman kai, sai in tafi Ƙasar Amurka. Jami'an shige da ficen nan suna Korar Jarumi daga cikin shahara ta".

16. "Ku rayu ayau, ba lallai bane ku hango hakan saboda matasan idanun ku, amma yanzu lokaci ne mai muhimmanci kamar yadda zaku iya samu a rayuwa. Saboda gobe duk mutuwa zamu yi".

17. "Babu wani Lokaci ko wuri da ya fi dacewa da soyayya, so shi bashi da Shekaru".

18. "Rayuwa tana farawa ne daga lokacin da muka yanke Shawarar cewa zata fara mana".

19. "Babbar Nasarar da na samu a rayuwa ita ce ina iya sanya mutane da dama murmushi ko da kuwa a jikin tallan Kamfanin Lux ne".

20. “gudu na ke a Gasar tsere su kuma mutane suna É—aya layin, tsere na ke yi da kaina".

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com


Post a Comment (0)