TAMBAYA TA 2,797

*Asssalamu Alaikum* . . *Tambaya ta 2,797:* = Munaso a tantancemana tsakanin sujuda qabali da ba'adi kuma sau daya ake sujudar ko sau biyu sannan sai anyi kabbara tare da daga hunnu ??? = = Amsa = = _Toh Sujuda qabli da ba'adi sune sujjadu guda biyu wadanda akeyinsu sakamakon samun rafkanuwa ko mantuwa kokuma shakka acikin sallah, Amma qabliyya itace sujjadu guda biyu wadanda akeyinsu bayan angama karanta tahiya kafin ayi sallama, kuma anayin kabbara kafin katafi sujjadar hakama idan zaka dago sai kayi kabbar dagowa amma ba'a sake maimaita tahiya bayan andago daga sujjadar tabiyu kenan tunda munce guda biyu akeyi, to da zarar ka dago kawai sai kadan zauna kadan sekuma kayi sallama base ka sake maimaita tahiyaba. Ita kuma Ba'adi yadda akeyinta shine bayan kagama karanta tahiya kayi sallama se kuma katafi sujjada tareda kabbara bawai sekayi kabbara daga zaunenba sannan kuma kasake tafiya sujjadar tareda kabbara, Aa kabbara daya zakayi seka tafi sujjada bayan ka dagoma zaka dagone tareda kabbara itama dai guda biyu akeyi kuma dazarar ka taso daga sujjada ta biyun seka dan zauna kadan kawai se kayi sallama batareda ka sake maimaita karanta tahiyaba wannan maimaita tahiyan kuskurene*****_ _Kuma babu laifi dan ka daga hannu yayinda kake kabbarar tafiya sujjadun dakuma sadda kake dagowa duk babu laifi idan ka daga hannu, hakama babu laifi idan baka dagaba, amma sedai wanda ya daga din yafi lada saboda hadisi ya tabbata Annabi (s.a.w) yace: kowanne daga hannu da mutum zeyi yanada lada goma, Qarin bayani gameda Ingancin hadisin sai aduba Taraju'atul Allamatil Albani, Mujallad na biyu idan ban mantaba****_ = = Allah yasa mudace . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . *مجلس تعليم الكتاب والسنة* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ . ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. . Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
Post a Comment (0)