TAMBAYA TA 42

TAMBAYA ========= 👇 Amincin Allah ya tabbata agareka mallam, Allah ya kara maka lpia da basira. Mutum ne JANABA ta kamashi ko kuma yayi mafarkin ya sadu da mace.Sa'annan washi gari da safe ana sanyi sosai kuma ba inda zai sami ruwan zafi domin yayi wanka,kuma inda yake ba turbaya ko dutse.Yaya zaiyi? Yana gidan sama ne mai hawa na biyar, kuma duk block ne da penti gashi kuma wajen akwai security ba daman ya sauko kasa, dan Allah malam ya zaiyi AMSA ===== 👇 Ae a jikin bango ko tiles ko Benci ma zai iyayin taimama matukar dai akwai kura akansa. Sabida haka ba sai a dandamalin kasa ba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)