TAMBAYA TA 2,799

*Asssalamu Alaikum* . . *Tambaya ta 2,799:* = Meye hukuncin kasuwancin da za'ace kakawo misali kamar dubu goma ahada na mutane dayawa ake kasuwancin canji,misali ake sayan kudin wata kasar idan yayi tsada se acanjar se araba ribar amma idan kakawo mutane dayawa za'ake kara ma wani abu akan naka ribar saboda kakawo mutane da yawa??? = = Amsa = = _Toh wannan irin kasuwancin bai halastaba kuma mafi yawan wannan irin kasuwancin 'yan Damfarane sukeyinshi se susaku kuyita gayyato mutane suna tara musu kudi dazarar kudin sunkai gejinda suke buqata sai su kulle shagon nasu su gudu subarku da rigima dan haka irin wannan kasuwancin bai halastaba****_ _Amma idan anaso ya halasta yadda za'ayi shine idan kowa yakawo kudinshi sai akira kowa yazo a zauna agindaya sharadi agaban kowa yaji cewa ga irin kasuwancinda za'ayu kuma za'a farashi daga lokaci kaza zuwa lokaci in Allah yasa angama akaci riba za'a rabata wane abashi kaso kaza wane abashi kaso kaza, shin kun amince?? Idan kowa yace ya amince bayan yasan menene abinda za'ayi kasuwancin kuma yaji irin kasonda zai samu daga cikin ribarda aka samu kowa sai yace yayarda ya amince sannan afara kasuwancin, inwani yace bai aminceba to kodai kucireshi aciki kubashi dukiyarsa kokuma kusan nayi. Sannan kuma bayan anyi kasuwancin angama akara kiran kowa yazo aware uwar kudin kowa ya tabbatar dukiyarsa tananan beyi asaraba, sannan idan ansamu riba to sai araba ribar da gwargwadon yadda kukayi wancan sharadin nafarko, inkuma bakuci ribaba shikenan kowa sai yarungumi qaddara. Hakama idan faduwa akayi uwar kudin bata fitoba nanma asarara tashafeku dukanku wannan shine yadda akeyin tarayyar kasuwanci na halal****_ = = Allah Yasa mudace . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . *مجلس تعليم الكتاب والسنة* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ . ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. . Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
Post a Comment (0)