TAMBAYA TA 46

TAMBAYA ======== 👇 Assalamu Alaikum malam Allah ya biya maka bukatunka duniya da lahira tambayata itace nakasance ina zuwa aiki wani local Gov. Daga cikin garin mu, kuma agidan iyayena nake saukato malam nakanje nayi kwana uku na dawo zan dinga yin kasarune kokuma zanna cika sallah na nagode malam. AMSA ====== 👇 Garin iyayenka ae ba nan bane garinku, inda kake da zama nan ne garinku, Sabida haka tinda aiki ne yake kaika, kaje ka dawo, Kasaru zakayi, idan ka dawo inda kake da zama da gidnaka da iyalinka anan ne zakake cika sallah. Saboda haka Kasaru zakana yi duk lokacin da kaje wannan local government din. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)