TAMBAYA TA 45

TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum, Mallam barka da warhaka, inaima fatan Alheri a koda yaushe. 💧Wani Babban malamine naji yana bada labari "waliyinsu in zaici abinci baya bismillah" da muridai suka tambaye shi ? Allah Karawa shehi daraja, Me yasa baka bismillah kafin kafara cin abinci? Sai yace : ai maganar babbace" Wallahi duk inda yake shaidan baya zuwa wurin, Domin kullum shi cikin ambaton Allah yake, kuma shaidan baya zuwa wurin ambaton Allah. 1)Mallam shin yin bismillah yayin cin abinci ba sunna bane? 2)Naji malamai sunce duk Wanda bai ambaci Allah ba tare da shaidan suke ci .to tayaya mutum zai gane baya tare da shaidan. 3)Mallam sannan wacce nasiha zakai ga masu irin wannan tunani? AMSA ====== 👇 Karya yakeyi, kuma ya rena musu hankali ma. Yana fito da jahilcinsa ne karara a fili, Su kuma suna fitar da wautarsu da rashin wayewarsu a addini kenan. Kasan duk wanda bai waye a addinance ba, komi ma ka gaya masa binka zaiyi. Har Akwai wadanda ma suke baiwa kansu matsayin Allah, amma kuma a kaiwa masu binsu. Ya kai ya manzon Allah saw daraja ne? To nasan ko farcen manzon Allah saw baikai daraja ba, amma manzon Allah saw idan zaici abinci sai yayi bismillah. Asali ma shine ya koyar da mutane yin bismillah kafin aci abinci, haka ya cewa da Abdullahi Dan abbas tin yana Dan karamin yaro, lokacin da yake cin abinci dasu, sai yaga yana cin gaban wani, kuma baiyi bismillah ba. Yace dashi, ya kai yaro, kayi bismillah, kaci gabanka, kuma kaci da damarka. Kuma duk walittakarsa ya kai sayyadina Abubakar? Amma idan Abubakar zaici abinci sai yayi bismillah. Haka duk inda yakai da shedan baya inda yake, ya kai sayyadina umar ne? Manzon Allah saw yace duk hanyar da sayyadina umar yabi, shaidan baya binta, amma idan sayyadina umar zaici abinci sai yayi bismillah. Kasan wadannan mutanen sai a hankali, yan cuwa-cuwar addini kenan,. Allah ya sawwake. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)