TAMBAYA TA 39

TAMBAYA ========= 👇 Dan Allah ka taimaka akan wata matsala ta iyali. Ya hukuncin jinin nifaas da ya wuce kwana arba'in? Mace zata jira kwana sittin yadda wasu bayanai 'suke nuni? Mlm asalamu alekum. Wai shin dolene tsarkin maziyin maza sai sun wanke gabansu duka? Allah karawa mlm lafiya amin. AMSA ===== 👇 Mace bazata jira Jinin haihuwa ko ya dauke Mata ba wai sai ta kai kwana 60 ba. Da zarar ya dauke Mata shikenan, koda a ranar da ta haihu ne jini ya dauke Mata zatayi wanka taci gaba da ibadun da Allah ya dora mata. Akwai wanda yace min idan matarsa ta haihu a ta dade wannan jinin ya kai kwana ukku. Sabida haka ya kamata mata su san wannan hukuncin. Kar jini ya dauke miki kuma ki zauna haka kawai bakya sallah da azumi. Maganar maziyyi kuma, idan ya zuba a jikin mutun sai ya wanke gabansa gabaki daya, kamar yadda yake wankewa idan yaje wankan janaba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)