DUK MACE NA BUKATAR SANIN WADANNAN ABUBUWA GUDA 6 KAFIN TA YI AURE
1. JIN DADI BA ZAI TABBATA BA A KULLUM
Rayuwar aure rayuwa ce da ta kunshi jin dadi da akasin haka. Matukar mace ta sa ma ranta cewa jin dadi da rashin sa duk za ta yi karo da su a cikin auren ta, hakan zai sa ta sama ranta salama, sannan ta zauna lafiya da mijinta saboda ta san ba kullum ne zasu kasance cikin jin dadi ba.
A ranakun da aka samu rashin jin dadi hakan zai bata kwarin gwuiwa na tsayawa mijinta ba tare da ta tuhume shi ba. Saboda bata da wannan dogon burin a rayuwar aurenta, duk yanda yazo matukar ba a shiga hakkinta ba ta kan jure tare da kauda kai.
Sannan ba za ta yi tunanin kullum sai mijinta ya faranta ma ta ba, ko kuma ya biya ma ta dukkan bukatunta. Sannan ta san cewa ba zai taba iya kyautata ma ta ba dari bisa dari.
2. DANGIN MIJINKI SUNA DA MATUKAR MUHIMMANCI
Iyayen miji da yan uwansa na da muhimmanci a rayuwar aurenki. Ki tafi da kyakkyawar zuciya a kansu, ki watsar da duk wani abu da mutane za su ce mi ki game da su. Ki bari har sai wani abu ya hada ku ta nan za ki san yanda za ki tafiyar da su cikin kwanciyar hankali.
Musamman iyayen miji da suka yi sanadin kawo abun kaunarki a duniya, ba ki da kamar su.
Duk yanda ku ka kai samun kwanciyar hankali da mijinki matukar kuna samun matsala da dangin mijinki, auren nan ya dinga tangadi kenan, ke kanki ba za ki samu kwanciyar hankali ba. Tun mijin na goyon bayanki za a zo lokacin da zai fara dora laifin a kanki.
3. BA KULLUM NE ZA KI JI YANAYIN SOYAYYA BA
Duk irin son da kike ma saurayinki, daga zarar kun yi aure akwai lokuttan da za su zo ki ji cewa ba ki jin wannan soyayyar, ba kuma wai dan kin daina sonsa ba. Ko da kuwa a ce duk duniya babu wanda ya kai mjinki wajen sauke duk wani hakkin da ya rataya a wuyansa sai kin ji wata rana kin wayi gari kina cikin wani yanayi sannan ba ki jin wannan soyayyar.
A’a yanayin kasancewarku a karkashin inuwa daya ne, kullum kuna ganin juna.
Za ku kwana ku tashi tare, wasu ma’auranta ma da wuya su yi kwanaki biyar basu ga juna ba. Jaridar “Times of India” ta taba wallafa labarin wasu ma’aurata da kan tafi aiki na wasu kwanaki basu tare, sun bayyana cewa a duk lokacin su ka dawo su kan ji su kamar sabbin ma’aurata hakan na sa soyayyar su kara karfi.
4. SAMUN SABANI ABU NE DA KE FARUWA, KUMA BA ZA A IYA GUJE MA SA BA
Mace ta sa ma ranta cewa dole a rayuwar aure a rika samun sabani, amma mi? Ki san matakan da za ki bi wajen magance wannan sabanin. A duk lokacin da a ka samu sabani, ke a matsayin ki ta mace ki saukar da kai, sannan ki samu lokaci na musamman wajen tattauna matsalolinku. Kowane aure da irin matsalolin da yake fuskanta da kuma yanayin yanda ake warware shi.
Ko da kuna da matsala iri daya da wata, yanda za ta warware ta ta matsalar ya sha bambam da yanda za ki warware ta ki, saboda kowane mutum da irin dabi’arsa.
5. A LOKACIN DA TAFIYA TA MIKA A LOKACIN NE KOMI KE DAUKAR ZAFI
A irin wannan yanayin wasu matan aurensu ke mutuwa, musamman tsakanin shekara daya zuwa biyar.
Akwai wata dabi’a ta mata a wannan zamanin ta rashin juriya, da kuma duk matsalar da ta tunkaro aure maimakon a magance ta sai kawai a nemo hanyar raba auren. Kalubale da matsaloli suna daga cikin ababen da ke kara ma aure karko, saboda a lokacin da suke faruwa a lokacin ake nemo hanyoyin warware su ake kara sanin juna.
6. ZAMAN AURE HAKURI DA JURIYA NE KE TAFIYAR DA SHI
Mafi yawan lokuta akan jaddada ma mace cewa aure ibada ce ta hakuri. Duk inda za ka zauna, zaman kuma ya wuce na mutum daya ya zama wajibi kayi hakuri, bare kuma rayuwa ta aure da kaso mafi yawa a ciki hakuri da juriya ne. Duk yanda aka kai ga kwatantawa mace yanda hakuri yake a gidan aure ba za ta fahimci mi ake nufi ba sai ta shiga daga ciki.
Duk yanda ku ka kai ga son junanku dole ku samu sabani a tsakanin wanda hakurin zai tafiyar da komi.
Babban dalilin da yasa aure a zamanin baya yafi karko da aminci kenan saboda hakurinsu, wanda yayi karanci a wannan zamanin, babban dalilin da ke kawo mutuwar aure..