TAYI WASIYYA DA RABIN DUKIYAR TA, SHIN TA INGANTACCEN?

*_TA YI WASIYYA DA RABIN DUKIYARTA, SHIN TA INGANTA?_*

                                *Tambaya*
Assalamu alaikum dan Allah malam tambaya nake yi akan wasiya, wata tsohowa ce ta rasu ta bar danta guda daya, sai kuma wani wanda ta rika tun yana jinjiri har ya girma sai tace: idan Allah yayi mata rasuwa a raba gidanta biyu a bashi rabi shima dan nata ya dauki rabin,  hakan ko ya halatta. ?

                                     *Amsa*
Wa'alaikum assalam, mutukar ba ta da wani gidan sai wanda ta yi wasiyya da rabinsa, To wasiyyar ba ta inganta ba, saboda Annabi ﷺ ya hana yın wasiyya da sama da daya bisa ukun dukiya, Ta bar danta mawadaci, ya fi ta bar shi yana maula a wajan mutane, kamar yadda hadisi ya tabbatar, a riwayar bukhari mai lamba ta: 3721.

Allah ne mafi sani

17\2\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)