*_ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA?_*
*Tambaya*
Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi, don zaman auranmu ya kara dadi ?
*Amsa:*
To 'yar'uwa wata mace ta je wajan Annabi ﷺ ta ba shi labari cewa: 'Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma gashi mijinta ya umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta iya karawa? sai Annabi ﷺ ya ce mata: A'a, saboda an la'anci masu kara gashi "Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4831.
Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa: bai halatta mace ta kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah.
Allah ne mafi sani.
22\4\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.