KURA-KURE GUDA 15 NA RANAR JUMA'A
1-Yin Addu'a da daga Hannuwa lokacin da Liman ya zauna tsakanin Hudubobi guda biyu.
*@ﺍﻟﻤﻨﺎﺭ "6/793-794ﻭ18/559*
2-Rashin yin Raka'a guda biyu na gaisuwar Masallaci wato *TAHEEYATUL MASJID* Lokacin da liman yake Huduba.
*@ﺍﻟﻤﺤﻠﻰ"ﻻﺑﻦ ﺣﺰﻡ 5/69*
3-Yin sallar nafila kafin sallar juma'a indai ba TAHEEYATUL MASJID ba,yin wata nafila kafin sallar juma'a da sunan nafilar sallar juma'a yin hakan kuskurene kuma bidi'ace.
*@ﺍﻟﺴﻨﻦ ﻭﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺎﺕ "51"ﺍﻟﻤﺪﺧﻞ" ( 2/239 )" ﺍﻷﺟﻮﺑﺔﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ "( ﺹ 20 - 33 )*.
4-Yin sakace wajan aikata manyan Ibadu na wannan rana mai albarka kamar:Karanta SURATUL KAHF da yawaita Salati ga Manzon Allah ﷺ a yinin juma'a da daren juma'a da rashin neman dacewa da lokacin amsa addua na wannan rana.
5-Jin kirta yin TAHEEYATUL MASJID lokacin shiga masallaci lokacin da ladan yake kiran sallah saboda amsa kiran sallah,yin hakan kuskurene,abinda yake daidai shine,kayi TAHEEYATUL MASJID sannan ka zauna ka saurari khuduba.
6-Rashin sanya Turare da rashin yin wanka da sanya tufafi mai kyau a ranar juma'a,abin kunya zakaga mutum idan zaije neman aure ya gyara komai kamar sabon sarki saboda budurwarsa abin yake gyara jikinsa saboda zuwa gani da Mahaliccinsa.
Zuwa masallacin juma'a da sauran masallatai bayan mutum yaci albasa ko Tafarnuwa kowani abu mai wari ba tare da ya gusar da sauarnan wannan warinba domin yin hakan yana cutar fa mutane da Mala'iku.
7-Rashin zuwa masallacin juma'a da wuri da rashin sauraran Huduba,wanda zuwa masallacin juma'a da wuri da sauraran Huduba da yin shiru lokacin huduba sune mafi girman aiyukan ranar juma'a bayan sallar juma'a.
8-Daga hannuwa lokacin da liman yake addu'a huduba sai idan yana adduar rokon ruwane alokacin hudubarsa.
9-Kuskurene ga wanda ya rasa ruku'u na raka'a ta biyu ta sallar juma'a da yayi raka'a biyu a matsayin sallar juma'arsa,abinda yake daidai shine yayi raka'a hudu ta Azzahar domin ya rasa sallar juma'a sai dai yayi sallar Azzahar.
10-Ketara tsakanin mutum biyu raba tsakanin mutum biyu dan ka zauna a gaban sahu,idan kanason zama a sahun farko kazo da wuri,yin hakan cutar da masu sallah ne kuma Manzon Allah ﷺ yayi hani akan hakan kuma yana janyowa mutum asarar Lada da kankare zunuban da akeyiwa mutum a ranar juma'a.
Domin Manzon Allah ﷺ yana Huduba a ranar juma'a yaga wani mutum yana ta ketara mutane sai Manzon Allah ﷺ yace masa;-
*(Zauna! Hakika kacutar kuma ka cutar)*
*@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ﻭﺻﺤﻴﺢ ﺍﺑﻦ ﻣﺎجه*.
11-Tsawaita Huduba da takaita sallah yana cikin kusakuran da limaman juma'a sukeyi,domin ka dadi kana huduba sannan kayi sallar a lokaci kadai ya sabawa abinda Manzon Allah ﷺ yakeyi kuma ya koyar.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Yana daga alamar fahimtar addinin Liman ya tsawaita sallar juma'a amma ya takaita Hudubarsa)*ana nufin ya tsawaita sallarsa ya takaita hudubarsa wannan alamace ta Fiqhun Liman,lallai daga cikin bayani akwai sihiri".
*@ﻣﺴﻠﻢ*
Daga Jabir Dan Abdillahi رضي الله عنه،yana cewa:-
*"Na kasance ina yin sallar Juma'a tare da Manzon Allah ﷺ yafi kowa kyautata sallar juma'a,Sallarsa ta kasance yar gajera sannan Hudubasa yar gajera"*.
*@ﻣﺴﻠﻢ*
12-Rashin zuwa sallar juma'a ba tare da wani uzuri ba na shari'a kamar mata da marar lafiya ko matafiya,kin zuwa sallar juma'a ba tare da daliliba yana bayya rashin kula da addini ga mutum da rashin daukar addini a matsayin komai,kuma hakan yana janyowa mutum mummunan karshi da fishin Allah.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Duk wanda yabar sallar juma'a har sau ukku,saboda sakace da lalace,Allah yayi rufi acikin zuciyarsa)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲّ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺣﺴﻨﻪ ، ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ، ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ ، ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻴﻬﻤﺎ ﻭﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ، ﻭﻗﺎﻝ :ﺻﺤﻴﺢ ﻋﻠﻰ ﺷﺮﻁ ﻣﺴﻠﻢ .
A wata Riwayar yana cewa;-
*(Dukkan wanda yabar sallar juma'a guda ukku ba tare da wani uziriba,to munafikine)*
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Kodai mutane su daina kin zuwa sallar juma'a ko kuma Allah yayi rufi a cikin zukatansu sannan mutum ya zama cikin gafalallu)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
13-Rashin yin nafila Juma'a bayan Juma'a a gida ko a masallaci bayan an fita daga masallaci an sake shigowa cikin Masallaci.
Daga Nafi'u daga Abdillahi dan Umar رضي الله عنها، ya kasance idan yayi sallar juma'a sai ya tafi zuwa gidansa sai yayi sallah raka'a guda biyu,sannan sai yace:-
*"Manzon Allah ﷺ yakasance yana aikata haka"*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.
14-Gafala da rashin neman dacewa da amsa addu'a a lokacin nan da Allah ya ware na musamman dan amsa adduar bayi a ranar juma'a.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Lallai a ranar juma'a akwai wani lokaci da babu wani da zai dace da wannan lokacin yana rokon Allah wani abu face Allah ya bashi wannan abu)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 852 ).
Wannan lokacin kuma yana nan akarshen yini na wannan ranar kafin faduwar Rana.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Ku nemi wannan lokacin a sa'a ta karshe a ranar juma'a bayan sallah la'asar)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ.
15-Yin surutu da hira lokacin Huduba da rashin sauraran Liman lokacin da yake Huduba.
Yin surutu lokacin Huduba haramunne kuma yana janyo mutum yayi asarar ladar Sallarsa ta juma'a kuma yin shiru da sauraran Huduba wajibine kamar yanda Manzon Allah ya kwadaitar.
Manzon Allah ﷺ ya fadi Falalar yin shiru da sauraran Huduba sai yace;-
*(......Sannan yazo sallar juma'a yayi Shiru ya saurari Huduba,an gafarta masa tsakanin wannan juma'ar zuwa wata juma'a da karin kwanaki ukku,Wanda ya goge kasa hakika yayi Lagawu)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ( 5/588 ).
Hakika magana lokain Huduba kuskurene mai girma koda abinda zaka fada a wannan lokacin Umarnine da kakkyawa da hani da mummuna to yin hakan a wannan lokacin Haramumne.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Idan kacewa dan uwanka yayi Shiru alhalin Liman yana Huduba a ranar juma'a to kayi Lagawu)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 851 ).
Allah ne mafi sani
*Allah bamu ikon gyarawa baki daya*