MIJINA YA SAKE NI INA SHAYARWA

*_MIJINA YA SAKE NI INA SHAYARWA, KO ZAN IYA IDDA DA WATA UKU???_* *Tambaya* Assalamu alaikum warahmatullah. Malam ga tambayata kamar haka watace akasaketa tana shayarwa kuma batayin al'ada toshin xata iya yin aure bayan wata uku ko kuma sai tajira ta yaye yaronta har taga al'adanta Kafin tayi auren nagode *Amsa* Wa'alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi shekara uku, kafin ta kammala iddar, saboda Allah ya rataye iddar matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila ba da jini uku, kamar yadda aya ta: 228 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani. 18/02/2018 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)