ZUNUBAI GUDA BAKWAI MASU HALAKARWA

*_ZUNUBAI GUDA BAKWAI MASU HALLAKARWA_* *Tambaya* Assalamu alaikum Mal. wadanne abubuwa ne guda 6 da Annabi yace mu gujesu suna hallakar da dan adam *Amsa* Wa'alaykumussalam, To dan'uwa abubuwan guda bakwai ne kamar yadda suka zo a hadisin Bukhari mai lamba: 6857 da kuma Muslim a lamba ta: 262, inda annabi ï·º yake cewa: ku guji abubuwa guda bakwai masu hallakarwa: 1. Shirka da Allah. 2. Sihiri 3. katshe rai ba tare da hakki ba 4. Riba. 5. Cin dukiyar maraya. 6. Juya baya a wajan yaki. 7. Yiwa mata katangaggu kazafi. Allah ne mafi sani. 5/3/2014 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)