SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI

*_SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI_* *Tambaya* Assalamu alaikum. Malam Don Allah menene fatawar malamai magabata akan shugabancin mata, kuma zan so ayi post mai zaman kansa akan wannann matsala. Allah ya taimaka. *Amsa* Wa'alaikum assalam Yawanci malamai magabata suna tafiya ne akan hadisin Abu-bakrah inda Annabi ﷺ yake cewa; "Duk mutanen da suka sanya mace ta zama shugabarsu, to ba za su rabauta ba" kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 4425. Don haka bai halatta ta rike shugabanci ba in ba na gidanta ba. Sannan malamai sun ce daga cikin hikimomin hakan shi ne: saboda raunin mace, da tawayar hankalinta, da kuma yawan tausayinta, sannan idan tana haila halayanta sukan canza, ka ga za ta iya yiwa mutane danyen hukunci. Ibnu Khudama yana cewa: "Annabi ﷺ bai taba sanya wata mace a matsayin shugaba ba, haka nan halifofinsa shiryayyu". Mugni 13\14. Duk lokacin da mutane suka dorawa mace shugabanci lamura za su tabarbare, kuma hakan har lahirarsu sai ya shafa, Shaukani yana cewa: "Babu wani narko da ya fi kore rabauta" Sailul jarrar 4\273. Allah ne ma fi sani. 21/10/2014 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)