*_YA MATSAYIN SHAFA AKAN SAFA YAYIN ALWALA?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam, tabayana akan shafar safa, innayi alwala da shafar zan iyayin sallah misali magrib da isha'i.
*Amsa*
Wa'alaykumus Salam.
Shafa a kan safa, wato جورب ko شراب a harshen larabci, a lokacin da aka zo yin alwala ya halasta bisa sharudda biyu:
1. Ya kasance an sanya safar ce bayan an yi cikakkiyar alwala, kuma ba cire ta ba, har lokacin da aka zo yin alwalar da a ke son a yi shafa a kanta.
2. Ya kasance ba a wuce yini da dare ba (kwana daya ko kuma salloli guda biyar) daga lokacin da aka sanya safar, idan a halin zaman gida ne, ko kuma kwana uku a halin tafiya.
A cikin *Sunan* dinsa, Imam Abu Daawud ya bayyana cewa an ruwaito halascin shafa a kan جورب (safa) daga Sahabbai fiye da guda goma. Shaikh Muhammad Naasiruddeen Albani ya tabbatar da ingancin ruwayoyin.
Idan mutum ya yi shafa a kan safar da ya sanya bisa sharuddan da aka bayyana a sama, zai ci gaba da sallolinsa da wannan alwala, matuqar ba ta warware ba.
Wallahu A'alam.
11/02/2018.
Rubutawa:- *_Dr. Ahmad Bello Dogarawa Zaria_*
Gabatarwa:- *_Ãbûbäkår Êkâ_*
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.