*_ZAN AURI KANWAR MATAR MAHAIFINA, KO YA HALATTA?_*
*Tambaya*
Malam ya halata mahaifina ya aure mace ,ni kuma na auri kanwarta.
*Amsa:*
To dan'uwa ya halatta ka aureta, saboda ba ta cikin mataye guda goma sha biyar wadanda Allah ya haramta a aure su a cikin suratunnisa'ai, ga shi kuma babu wani hadisin da ya haramta a aure ta, Allah yana cewa a cikin suratunnisa'i aya ta: 24, bayan ya ambaci matan da aka haramta a aura, "Duk matan da ba wadannan ba, to an halatta muku ku aure su.
Allah ne mafi sani
10\3\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.