ALLAAH YA BAMU SHUGABA NE DAI DAI DA MU

Idan kana son ka gane cewa mu Talakawan Nigeria Allah ya zaɓa mana shugabanni daidai damu ne, ba zaka sha wahala ba!

Daga Abubakar Mansur Daura

Duk wani masallaci za kaga an yima Amplifier keji, da rodi an saka makulli an rufe.

Dai dai da Agogo sai an mata keji an saka makulli an rufe, Saboda gudun Sharrin Talakan Nigeria.

Generator wanda yake baiwa masallacin wuta sai an masa cikakkiyar adana tare da saka masa kacha asa makulli a kulle a wasu guraren Saboda gudun sharrin Talakan Nigeria, a hakan duk ba'a tsira ba ana sa ran za'a iya sacewa!

Babu Masallacin da zaka cire takalmin ka masu kyau ka barshi a qofar shiga Masallacin zaka koma gida da qafarka haka kuwa don za'a sace maka shi.

Babu wa'azin da yakai mutuwa idan kaje maqabarta gawarwaki ne kwakwance tsofaffin kushewa da sababbi yara da manya maza da mata, amma Talakan Nigeria har a maqabarta be daina yin sata ba, Yana maimaitutuwa a baiwa mutum Amanar riqon wayar Salula ya hana ya riqe wayar ayi cikiyar duniya ba zaka ji wanda yace ga waya.

Wanda yayi sata a maqabarta ko masallaci dan Allah wani abune bazai iya aikatawa na laifi ba

Idan damina tazo ka gwada yin Noma inba sa'aba kafin ka ankara wani yazo ya rore maka wake ko ya yanke maka hatsi.

Saboda satar mashin Talakan Nigeria yana yima mutum yankan rago saboda ya qwace ma wani mashin kawai

Lebura mai yin gini zai sace Simintin da suke yin gini don ya sami kudi saboda tsabar ha'inci, Kanikawa ma hakan take.

Malaman makarantun kwana idan an kawo musu abincin É—alibai daga gomnati su sace abincin su sayar da wani su kai wani gidajensu su dinga ci da iyalansu, Idan magani aka kawo domin É—alibai su sace su saya

Ka bude shago ka dauko wani talaka bayan ka zuba hajah ka dora shi a kan dukiyar ka kaga yadda zai ci amanar ka.

Azumin watan Ramadana yana dab da zuwa 'Yan kasuwa Musulmai zasu qara ma kayan masarufi tsada saboda Musulmai su shaa wahala dan kawai su sami kudi.

Amma a haka muna son shugabanci ne irin Shugabancin Qasar Saudiyya, Yadda mu Talakawan Nigeria halin mu da É—abi'un mu, suke Irin hali da É—abi'un Talakawan Qasar Saudiyya ne garemu?

Duk yawan mu bamu kai 'yan China yawa ba amma suna jin dadin rayuwa, Yadda Talakawan su suke haka shugabannin su suke, Allah baya zalinci!!!

Duk me son ya girbe dawah to ya shuka dawah ba yadda za'ayi mu talakawan Nigeria mu kasance:
Barayi
Maha'inta
Marasa tausayi
Marasa kishin qasa
Sai kuma Allah ya bamu shugabanni ba barayi maha'inta masu kishin qasa, marasa mugunta ba!!!

In banda Allah mai tausayin bayinsa ne, Allah ya tausaya mana ma tunda ya bamu shugabanni irin wa'yannan wanda idan zalincin su yafi haka be kamata muce komai ba saboda shugabannin yadda suke haka muma muke, wani lokaci gara halin shigabannin ma bisa ga halin mu.

Ba lokacin da mu talakawa muke tuhumar kanmu kullum tuhumarmu kan shugabannin mu take tsayawa bayan mune silar samuwan Azzaluman Shugabannin saboda zalincin mu, Idan Talakan Nigeria ya sami wata dama zalincin da zaiyi Wallahi wasu shugabannin ma ba zasu yi ba!

Bamu da aiki sai yawan qorafi kan shugabanni kuma munqi mu gyara namu matsalolin matsalolin shugabannin mu muke leqe muke hange, a haka zamu zauna cikin qasqanci da wulaqanci matuqar bamu sauya daga yadda muke ba, haka shima Allah ba zai sauya mana ba!

Idan da wanda ya san wata qasa a duniya wacce talakawa suke aikata irin abinda mu Talakawan Nigeria muke Aikatawa kuma Allah yabasu Shugabanni masu kirki ya fada mana wannan qasar a duniya muji, wacce qasa ce???

Dan uwa zan baka Assignment ka zauna kai kadai kayi tadabburin duk wata qasa a cikin wannan duniyar Wallahi za kaga yadda Talakawan Qasar suke haka Shugabannin su suke Allah baya zalinci, Duk gonar da aka shuka shinkafa to shinkafar za'a cire, Yadda ba wanda ya taba noma Doya ya tono Dankali, haka zalika ba yadda za'ayi Talakawan Nigeria a irin mayagun É—abi'un mu Allah ya bamu shugabanni ba masu mayagun É—abi'u ba!

Mu Talakawan Nigeria mun mai da Al-amarin gyaruwar Nigeria ne kan Shugabannin mu su kadai mu banda mu, a haka muke son qasar ta gyaru ba tare da gudun mawar mu ba.

Shi yasa qasar take yadda take jiya yau Wa'yanda suke Mulkarmu a yau idan muka duba ba wasu sababbi bane wa'yanda suka mulki iyaye da kakannin mu sune yau suke mulkarmu har yanxu ba sauyawa akayi ba, Gobe da jibi sune zasu mulki 'ya'yanmu da jikokinmu idan sun mutu 'ya'yansu ne zasu ci gaba da mulkar mu, Munxo a gyara zamu koma a Allah koro, Idan baka gane ba yanxu da nake magana waye Gomnan garin ku? Su waye komishinonin? Su waye 'yan majalisun jahar, su waye chiyamomin? Duk zakaga kullum dasu ake damawa haka abin yake har a matakin Gomnatin Tarayya, tun daga kan Shugaban qasa zuwa qasa duk wani muqami za kaga daga tsohon gomnan jiha kaza sai tsohon ministan kaza, sai tsohon dan majalisa kaza har yanxu sune ke riqe da muqaman a ko wanne mataki na Gomnati, Talakawan Nigeria Qalu Balen mu Wallahi idan bamu gyara ba haka qasar zata ci gaba da tafiyar Hawainiya Jiya tafi yau Yau tafi Gobe.

Yaa Allah ka gyara mu ka bamu ikon gyara hali da É—abi'uun mu Ameen Alla
h ya shiryar da Shugabannin mu suma su gyara Ameen.
Post a Comment (0)