TAMBAYA
========
👇
Assalamu Alaikum dafatan malam ya wuni lapia Allah y kara lapia da imani Aameen. Malam Tambaya shine nakasance idan nayi fitsari ina dadewa kafin ya dauke gaba daya saiyayi kaman ya kare sai wani kadan yafito to malam wani lokaci innazo sallah sai naji kaman ya fito toya matsayin sallahna tunda inajiransa kusan minti 5 Allah ya kara basira.
Malam mutumne yana sallah sai Akwai yaro agefensa sai yaron ya dau wuka ko zai fado a gado shin xaa iya karban wukan koa saukeshi a gado ko zaa yanke sallanne.
AMSA
======
👇
Na farko dai akwai Alamar shaidan yana neman yimiki wasa da Addininki gaskiya, inaga kamar yana neman ma ya hanaki bautawa mahallincinki ne.
Nan gaba abinda zakikeyi, wato idan kin gama fitsari, karkiyi tsarki, har sai kin tabbatar da cewar wannan Fitsarin ya tsage, harma wasu malaman fiqhu suna ganin, idan mace tayi fitsari, kai tsaye bazatayi tsarki ba, har sai ta danyi yunkuri kamar zata mike tsaye, sai ta koma ta tsuguna, idan ma akwai wani fitsarin zai fita, sai tayi tsarki kawai, koda kuma taji wani Abu, bayan tayi tsarki karta damu ba fitsari bane, shaidani ne yake mata wasa da sallah.
Sannan duk lokacin da mutum yake sallah, idan yaga wani hadari zai faru, ya zama wajibi ya katse wannan sallar ya kai agajin gaggawa, daga baya sai yazo ya sake wannan sallar.
Sabida haka nan gaba tinda wannan ya wuce, dole ne ki karbe wannan wukar, haka zalika ga wanda yaga makaho yana tafiya gashi zai fada rijiya, Alhalin kana sallah, dole ne ka katse wannan sallar ka ceci wannan makahon.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 0810860
5876