MECECE KUNYA?

TAMBAYA
========
👇
Mal. Inada tambaya?
Allah yabada ikon amsawa Ameen
 Minene kunya?
 Minene alamomin kunya?
 Ya ake gane maras kunya?
Allah yabada ikon amsawa Ameen


AMSA
======
👇
1. Kunya tana da ma'anoni da yawa.
Misali, kunya tana nufin kawaici, tana nufin rashin saka jiki ga wani wanda kake ganin girmansa Ko wanda ya fika shekaru ko ilimi, da dai sauransu.
2. Alamar kunya shine buya da sunkuyar da kai da rashin yadda ka hada ido da wani ko wata.
3. Maras kunya shine wanda baya ganin girman kowa kuma a wurinsa ba wani abu bane dan wani ya ganshi yana aikata wani abu wanda bai dace ba.
 Misali. Duk wanda zaka ganshi yana yana sha kayan maye ko ya riko taba cigarette yana sha a idon mutane, da Alama bashi da kunya, ko idan kaga mace tayi shigar banza, kuma tafiya a idon mutane ba a gidansu ba, anan ma wannan matar bata da kunya.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZ
A MATA 08108605876
Post a Comment (0)