MENENE AINAHIN TSORON ALLAAH

MENENE AINAHIN TSORON ALLAH?

Tsoron Allah ba wai yana nufin sanya dogayen kaya, Ko Sanya rawani, Ko rike charbi, ko ajiye gemu, ko sanya dogon Hijabi bane. Ba kuma yana nufin yin siffah irin ta Malumta bane. MashaAllah, duka wadannan halaye da dabi'u na gari ya na da kyau..

Amma !!!

Tsoron Allah yana nufin BARIN SA'BON ALLAH saboda Jin tsoron gamuwarka dashi, Da kuma bin Allah sau da Qafa don kwadayin samun rahamarsa.

Tsoron Allah yana nufin ka rika jin kusancinsa gareka ako yaushe, aduk inda kake.

Daga cikin masu tsoron Allah daga magabata na kwarai, akwai wanda ya sanya hannu cikin bakinsa, ya Qakaro amai, ya amayar da dukkan abinda ke cikin cikinsa saboda wata lauma guda da ya hadiya wacce bai san asalinta ba.

Akwai wanda yayi tafiyar fiye da Mil Hamsin a Qafa domin mayar da wani alkalamin da ya karbi aronsa awajen abokinsa, ya taho dashi bisa mantuwa.

Akwai wata matar da ta rayu fiye da shekaru arba'in bata yin magana da kowacce kalma sai ta Alqur'ani.

Tsoron Allah shine zai sanya ka rika jin bakin ciki da damuwa acikin zuciyarka idan ka rasa Jam'in sallah sau 'daya rak!

Tsoron Allah shine zai sanya idan kana azumi, yadda bakinka ya kaurace ma abinci, hakanan dukkan gabobin jikinka zasu kaurace ma dukkan wani nau'i na sa'bon Allah.

Tsoron Allah shi zai sa ka nemi yafewar dan uwanka wanda ka zalunceshi acikin magana ko aiki.

Tsoron Allah shi zaisa barci ya gagareka saboda tunanin wani mummunan abu da ka aikata yanzu ko tun da dadewa.

Tsoron Allah shi zai sa ka rika runtse idonka daga kallo, ji ko saurare da furta haramun. Kuma shi zai sa ka kauce daga kadaituwa da haramun....

Tsoron Allah shi zai sa kullum ka rika kauce ma bin son zuciyarka na sha'awa ko son tara abin duniya.

Tsoron Allah shi zai sa ka rika tsarkake zuciyarka acikin dukkan abinda zakayi.

Tsoron Allah shi zai sa ka kiyaye harshenka daga abaton da gibar Jama'a ko gulmarsu ko cin mutuncinsu, ko yin mummunan zato garesu.

Tsoron Allah shi zai sa ka kiyaye dukkan gabobin jikinka daga aikata sabonsa komai kankantarsa.

Tsoron Allah shi zai sa ka kiyaye kanka daga zaluntar bayinsa, Sannan ka rika yin afuwa garesu koda sun zalunceka.

Tsoron Allah shine Shugaban dukkan halayen Kwarai, Kuma dashi ake samun dukkan abin nema.

Allah madaukakin sarki yana cewa:

"HAKIKA ALLAH YANA TARE DA MASU TSORON ALLAH, DA KUMA WADANDA SUKE KYAUTATAWA".

Kuma yace:

"DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO (ALLAH DIN) ZAI SANYA MASA MAFITA (DAGA DUKKAN QUNCI).

Kuma yace :

"DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO (ALLAH DIN) ZAI KANKARE MASA ZUNUBBANSA KUMA ZAI GIRMAMA MASA LADANSA".

Kuma yace:

"DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO (ALLAH DIN) ZAI SANYA MASA SAUKI ACIKIN AL'AMARINSA".

Ya Allah ka sanyamu cikin bayinka masu jin tsoronka ako yaushe, a kowanne lokaci, kuma aduk inda m
uke.

Ameen.

Allah yasa mu dace da rahamar Sa

Ameen
Post a Comment (0)