MENENE HUKUNCIN RAGE GEMU A MUSULUNCI?

*MENENE HUKUNCIN RAGE GEMU A MUSULUNCI ?*

*TAMBAYA*

Assalamu alaikum warahamatullah malam Allah ya karama lafiya malam ina neman Karin bayani akan rage GEMU

 *AMSA*

 Wa alaikums salam hakika manzon Allah S.A.W. yayi umarni da cewa kada a rage gemu akwai hadisai sahihai ingantattu masu tarin yawa wanda Annabi s.a.w. yayi umarni yace ku cika gemu sannan Ku datse gashin baki domin ku sabawa majusawa A shari'ar musulunci ba'a yadda mutum ya cire gemu ba Amma babu laifi zaa iya gyarasa idan ya zama babu kyan gani za'a iya tsaftacesa a gyarasa wannan ba laifi bane amma a sanya almakashi a rage masa tsawo wannan ba dai dai bane kuma kuskure ne sai dai idan yakai (DUNAL KABDA) Ma'ana gemun tsayinsa yakai damki guda ma'ana idan kasa hannunka ka rikesa abinda yayi saura wasu malamai suna ganin babu laifi zaka iya ragesa amma galibi mu gemu nanmu basa kai yawan haka ba don haka ya kamata a sani gemu addini ne kuma kwarjini ne domin gemu sunnar Annabi S.W.A. ne kuma gemu shine yake bambamta tsakanin namiji da mace Allah shine mafi sani

 *Amsawa✍*

 *DR ABDALLAH GADON KAYA
*
08/03/2017
Post a Comment (0)