HUKUNCIN DAGA HANNU A LOKACIN ADDU'A

*HUKUNCIN DAGA HANNU LOKACIN ADDU'A*.

*​Tambaya:​*
Assalamu alaikum mallam ina da tambaya mallam ya halarta kana addu a kana ronkon Allah ka daga hannun ka sama?



Wa alaikumus salam.


*​Amsa:​*
Eh lallai ya halatta mutum ya daga hannunshi lokacin addu'a, hadisai da yawa sun nuna hakan kamar hadisin da annabi s.a.w ke cewa " lallai ubangijinku mai kunya ne mai karamci ne yana kunyar bawa ya daga hanunshi ya roqeshi amma ya mayar dasu batare da komai ba" haka manzon Allah ya lissafa daga hannu yayin addu'a cikin sabbuban amsa addu'a, dan haka ya halatta, sai dai inda manzon Allah bai daga hanu ba bazamu daga ba, kamar lokacin da liman ke hudubar juma'a, ko tsakanin sujjada biyu, kenan inda Annabi s.a.w ya daga zamu daga, inda bai daga ba bazamu daga ba, a addu'oinmu na yau da gobe zamu daga matuqar shari'a bata hanamu ba.


*​Allah ne mafi sani​*


*​Amsawa:​✍🏻*
ABDULLAHI ISMAIL AHMAD.

29/04/2018

Zauren Fiqhul Usrah 0814
9690671 whatsapp
Post a Comment (0)