*_AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI?_*
*Tambaya?*
Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci.
Malam matsala ta haihuwa gareni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata ta rikice sai yazo yau bazan sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na nkeyi na cigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara?
Sai kuma da watan Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yayi min wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin nawa yake?
*Amsa:*
Wa'alaykumussalam, To 'yar'uwa Allah Madaukakin sarki a cikin alqur'ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah da azumi ba.
Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al'ada, wannan yasa barin su shi ne yafi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa.
Allah ne mafi sani
Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa.
Gabartawa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.