BEBE YAYI MAGANA

BEBE YAYI MAGANA ***************************** Daga ummu jundabi tace ta ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassallam, wata mata tana beye dashi daga haisami a tare da ita akwai wani yaro wanda baida lafiya (bebe) / sai tace Ya Rasulullah ! Haqiqa wannan yaro nane shiyayi saura a ahlina gashi baida lafiya baya magana / sai Manzon Allah SAw yace A zo mashi da ruwa ! Sai aka zo mashi da ruwa ya wanke hannun shi sannan ya kuskure bakin sa sannan ya bata / yace ki bashi yasha sannan ki yayyafa masa ki nime Allah ya warkad dashi. / sai ummu gundabi tace sai bayan anyi shekara na hadu da wannan mata data kawo yaro wajen Annabi SAW SAI na tambaye ta akan yaron / sai tace ai ya warke ya zama mai cikakken hankali (kwakwalwa) fiye da sauran wasu mutane dayawan gaskee / Allah ya qara mana muhabba da kusanci da taraqqe da wuddu da shagafu da fana'i cikin Ma'aiki SAW ameen x 99 x 189 / Duba mu'ujizatul rasull (dubu) mu'ujiza ta 354 shafi na 187

Post a Comment (0)