YA KASHE MATAR SA

YA KASHE MATARSA
Wata mata ce mijinta yayi mata kishiya sai uwargidan ta shirya kashe amaryar idan dare yayi suna kwance inji Sa'ad khalifa yakubu Sky don haka da dare yayi sai uwargidan ta sami wani kulki ta la6a6a cikin dakin amarya da aka sakaya ashe mijin na ciki yana lazimi sai yaga mutum da kulki ya shigo cikin dakin amaryarsa sai ya zata 6arawo ne saboda shigar maza da uwargida tayi don 6atar da kamanni. Don haka sai mijin yayi wuf ya chafke kulkin hannun uwargida suka kama kokawa har Allah Ya bashi sa'a ya dabaibayeta ya daga sama ya fyada da kasa har kanta ya rabe biyu nan take ko shurawa ba tayi ba ta mutu murus.
Da aka je wajen mahukunta sai shari'a ta wankeshi sumul luqwi a matsayin 'yar ta'adda ya kashe a bisa kariyar kansa da iyalinsa.
TOH HATTARANKU DAI MATA DA ZAFIN KISHI.

Post a Comment (0)