Da Masu hankali Nake

DA MASU HANKALI NAKE! Zuciya wata rumface yalwatacciya, wacce ta tattara soyayyar ma'abota kyautatawa da nagarta agareta, babu wata zuciya da bata ajiye soyayya a cikinta, saidai matakan soyayyar yakan banbanta, kada wata zuciya ta rudeka da cewar kai kadai take so ko take tunani, amma xata iya cewa kai kadai tafi so da tunani. Yaku ma'abota zukata! Kada ku sadaukar da zukatanku ga kowa face ubangijinku, domin shine kadai cikakken mai kulawa da bukatun zukata. Kuma babu tsoro ko bakinciki ga masu tsantsar soyayya ga ubangijinsu. Tabbas kaskanci da walakanci sun tabbata ga mai take hakkokin ubangiji bisa ganganci, kuma tuba da gyara ayyuka shine suturar ma'abota hankali.

Post a Comment (0)